
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gabannin rasuwarsa, sanannen Attajirin Ɗan kasuwa, Aminu Alhassan Ɗantata ya ce ya daina jin daɗin rayuwa duk da arziƙin da Allah ya ba shi, don haka yana fatan ya cika da imani.
A ranar Asabar aka sanar da rasuwarsa bayan ya shafe shekaru 94 a duniya, kusan shekaru biyu da rabi da furta kalaman nasa.
Ɗantata mai shekaru 91 a lokacin, ya faɗi haka ne yayin da ya karɓi baƙoncin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a wancan lokacin, Kashim Shettima.
Ya ce, tun daga yaranta ya haɗu da mutane da dama wanda a saboda haka ya ke da abokai a kowace jiha a Nijeriya, saidai abu ne mai wahala a samu guda 10 daga cikinsu a raye.
“Gaskiya, a yadda nake yanzu, ina jiran lokacina ne. Na daina jin daɗin rayuwa yanzu. Ina fatan na bar duniyar nan da imani”, ya ce.
Ya kuma ce, “Ina fatan ban ɓata wa kowa ba a rayuwa. Idan na ɓata wa wani, ina fatan ya yafe mun. Idan wani ya ɓata mun, Na yafe masa”, inji Ɗantata.
“Ni kaɗai na rage a gidanmu, inda na ke rayuwa da jikoki,” inji shi.
Marigayin ya yaba da ziyarar da kuma yi wa Nijeriya addu’ar fatan samun zaman lafiya mai ɗorewa.
