
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Sa’o’i bayan tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar LP, Peter Obi ya soki tafiye-tafiyen Shugaba Bola Tinubu na kwanan nan zuwa ƙasashen waje, Fadar Shugaban Ƙasa ta yi bayani game da zuwan Tinubu Saint Lucia.
A ranar Asabar Tinubu ya bar Abuja da nufin zuwa ƙasashe biyu da suka haɗa da Saint Lucia da taron BRICKS karo na 17 a Rio de Janeiro dake Brazil wanda za yi a ranakun 6 da 7 ga watan Yuli.
An samu sanarwar ne a wata takarda daga kakakin Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga.
Saidai, da ya ke tsokaci akan lamarin, Peter Obi ya bayyana tafiyar Shugaban Ƙasar a matsayin abinda aka yi da nufin holewa da shaƙatawa..
Obi, wanda ke ƙoƙarin fahimtar yadda alƙiblar jagorancin ƙasar ya ke, ya ƙalubalanci yanayin tafiye-tafiyen Shugaban ƙasar musamman duba da halin buƙatun gaggawa da ƴan ƙasar suke neman a biya musu.
Jim-kaɗan bayan haka ne Kakakin Tinubu, Fredrick Nwabufo ya fitar da bayani dalla-dalla game da batun tafiyar, inda ya kare shi da cewa ya je ziyarar aiki ne domin gina alaƙa mai ƙarfi tsakanin Nijeriya da ƙasashen yankin Caribbean.
Ya kuma ce, an yaɗa batun zuwan Tinubu ƙasar a kafafen yaɗa labarai da dama har da makarantu a ƙasashen yankin.
