
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Alhamis ne Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC) ta ƙi amincewa da buƙatar da tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello ya gabatar wa kotu domin ba shi damar fita ƙasar waje neman magani.
Babban jami’in hulɗa da jama’a na EFCC, Dele Oyewale a wata takarda da ya fitar ranar Juma’a, ya ce an miƙa takardar buƙatar ne a yayin cigaba da sauraron ƙarar zargin Yahaya Bello da hannu a badaƙalar Naira biliyan 80.2.
Lauya mai kare tsohon gwamnan, J.B. Daudu ya nemi kotun da ta amince da buƙatar wanda ya ke karewa duba da muhimmancin kiwon lafiyarsa.
Ya kuma ce, a tsawon shekaru takwas Bello bai yi wata tafiya zuwa ƙasar waje ba, wanda a yanzu ya ke matuƙar buƙatar a ba shi damar fita cikin gaggawa domin kula da lafiyarsa.
Haka kuma, lauyan ya ce tsohon gwmanan bai da rahoton aikata manyan laifuka a ƙasashen waje, don haka babu barazana game da tafiyar tasa.
Saidai duk da haka, Lauya mai kare ɓangaren EFCC, wadda ta shigar da ƙarar tuhumar, Kemi Pinheiro (SAN) ya ƙalubalanci hakan a inda ya ce ya saɓa wa ƙa’idodi da sharuɗɗan ayyukan kotu.
Pinheiro ya ce, Yahaya Bello a baya, ya miƙa irin buƙatar a wata kotun da babbar kotun Abuja, sannan kuma a yanzu ya sake zuwa wannan kotun da batun, lamarin da ya ce bai dace ba kuma akwai rikitarwa a ciki.
