Babu sadaukarwar da za ta yi yawa domin samun zaman lafiya a Ribas- Fubara

Spread the love

Daga USMAN KAROFI a Abuja

Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya bayyana cewa babu wata sadaukarwa da za ta yi yawa idan ana ƙoƙarin samun zaman lafiya, kwanciyar hankali da cigaban jihar. Yayin da yake jawabi ga magoya bayansa a birnin Fatakwal a ranar Asabar, Gwamna Fubara ya tabbatar musu cewa duk wani mataki da ya ɗauka, ciki har da sulhu da ya yi da tsohon gwamnan jihar kuma ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, an yi ne da la’akari da muradunsu na bai ɗaya.

Fubara ya fahimci cewa akwai magoya baya da ke cikin damuwa da rashin jin daɗi game da sulhun da aka cimma, amma ya jaddada cewa lokutan wahala suna buƙatar ɗaukar matakai masu tsauri da haƙuri. Ya bayyana cewa ba da kansa kaɗai ya yanke shawarar sulhun ba, domin a kowane mataki an gudanar da shawara da masu ruwa da tsaki da kuma aminan siyasa.

Gwamnan ya bayyana cewa sabbin sauye-sauyen siyasa na iya zama masu raɗaɗi ga wasu daga cikin masu biyayya gare shi, musamman waɗanda suka tsaya tsayin daka a lokacin rikici. Amma ya ƙara da cewa babban burinsa shi ne ganin jihar Ribas ta samu zaman lafiya da cigaba mai ɗorewa . Ya kuma nuna yadda rikicin siyasa ya janyo tsaiko ga wasu ayyukan raya ƙasa a faɗin jihar.

Duk da haka, Gwamna Fubara ya bayyana fatansa cewa sulhun da aka cimma zai taimaka wajen farfaɗo da ayyukan gwamnati da kuma hanzarta aiwatar da su. Ya kuma jaddada rawar da Shugaba Bola Tinubu ya taka wajen sasanta tsakaninsa da Wike, yana mai kira ga magoya bayansa da su rungumi zaman lafiya, su dage da goyon bayansa domin ganin jihar Ribas ta kai matsayin da ya dace da ita.

By ukarofi