Zamfara: Iyalan marigayi ‘Yandoto sun nemi Gwamna Lawal ya sa baki domin a yi masu adalci

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Iyalan marigayi Magaji Lawali ‘Yandoto da aka yi wa kisan gilla a bara da ake zargin tsohon kwamandan hukumar kare haƙƙin al’umma ta jihar Zamfara ZCPG, Kanal Rabiu Yandoto Rtd yayi, sun roki gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal da ya sa baki a kan lamarin domin a yi masu adalci.

Ɗaya daga cikin ɗansa, Anas Magaji Lawali ne ya yi wannan kiran a wani taron manema labarai a Gusau.

A cewarsa, belin wanda ake zargin Kanar Rabiu ‘Yandoto Rtd ba tare da tuntuɓarsu ba da kotun da ke zamanta a Gusau ta bayar ba tare da wani sharadi ba, ya haifar da rashin tabbas a tsakanin iyalan ko za a iya yin adalci a kan lamarin.

Ya ce, tuni suka rubuta wasiƙa ga gwamnan jihar ta hannun babban mai shari’a na jihar kuma kwamishinan shari’a domin sa baki cikin gaggawa kamar yadda gwamnan ya yi alƙawari tun da farko cewa dole ne a yi adalci.

A cewarsa, a ranar 12 ga watan Agustan 2024, kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara ya kama tare da binciken wanda ake zargi da kisan mahaifin nasu watau Kanar Rabiu ‘Yandoto rtd.

Ya cigaba da cewa bayan kammala binciken da ‘yan sanda suka gudanar, an samu hujjar farko a kan Kanar ‘Yandoto cewar shine ya yiwa mahaifinsu kisan gilla, kuma an gabatar da shi a gaban babbar kotun majistare (CMC) dake a Gusau inda kotu ta bayar da umarnin tsare shi a gidan yari na Gusau.

“Kotu ta bayar da umarni ga ofishin babban mai shari’a da ya gurfanar da wanda ake tuhuma a gaban kotun da ke da hurumin sauraren ƙarar cikin wa’adin da aka ƙayyade”.

Ya kuma ƙara da cewa hakan bai samu ba daga ofishin babban lauyan jihar Kuma kwamishinan Shari’a, wanda hakan ya sa kotu ta bayar da belin wanda ake ƙara.

“Abin takaici tun lokacin da aka bayar da belin babu wani mataki da babban mai shari’a na jihar ya ɗauka na gurfanar da wanda ake tuhuma a gaban kotu shi ya sa muke buƙatar gwamna Dauda ya sa baki.” Yace

“Muna neman gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya sa baki wajen ganin an gurfanar da wanda ake tuhuma idan akwai wata ƙara ko amsa a gaban kotun da ta dace”. Yace

A cewarsa, Marigayi Magaji Lawali ya bar yara 23 musamman ‘yan ƙasa da shekaru, yana mai cewa rayuwa na ƙara musu wahala wajen jurewa mutuwarsa da ba za a iya misalta shi ba.

“Kamar yadda nake magana a yanzu, mu 23 ne mahaifinmu ya bari bayan yi masa kisan gilla, Kuma daga cikin mu 21 yara ne masu ƙarancin shekaru kuma tun bayan kisan gillar da aka yi masa, rayuwa ta ƙara dagulewa, kuma muna buƙatar adalci a kan wannan lamari”. Yace

Idan dai za a iya tunawa, a watan Agustan shekarar data gabata ne jami’an tsaron al’ummar Zamfara CPC suka kai farmaki gidan marigayin dake garin Yandoto inda suka kamashi tare da da tsare shi a ofishinsu da ke ƙaramar hukumar Tsafe kuma ya mutu bayan kwana ɗaya a hannunsu.

By ukarofi