Daga AISHA ASAS
‘Idan ka na so ka ga martabar mutum, ka duba irin ayyukan alherin da ya bari a bayansa’
‘Ba a kwatanta mutum da kujerar da ya ke kai, sai dai da irin hatsin da ya girbe a zukatan jama’a.’
Wataƙila hankalin mai karatu zai tafi kan tunanin cewa wannan rubutun wani yunƙuri ne na yabo don neman wata lada ko ɗaukaka darajar wani mutum kamar yadda wasu sukan yi a koda yaushe. Idan kuwa can hankalinka ya karkata, ina mai baka haƙuri, ya kai mai karatu, domin wannan rubutu ya nisanta daga irin wannan ɗabi’a.
Za ka iya yarda da ni idan ka tambaya, shin wane ne Malam Lawal Maidoki? A lokacin ne za ka gane cewa, idan ka ji wane to fa ba banza, domin ko ba a sha dare ba, an sha rana. Wannan ne ya sa yabon gwani ya zama dole.
A daidai lokacin da ake fama da ƙuncin rayuwa, rashin aiki, talauci da ɗimbin ƙalubale da suka dabaibaye al’umma musamman a Arewacin Najeriya, akwai wasu ‘yan tsirarun mutane da ke fitowa da haske tamkar taurari a cikin duhu. Daga cikin waɗannan mutane, babu wanda ya fi ɗaukar hankalin al’umma da girmamawa kamar Malam Lawal Maidoki, wanda jama’a suka fi sani da Sadaukin Sakkwato, wani laƙabi mai nauyi da ya dace da nagartarsa.
Sunan ‘Sadaukin Sakkwato’ ba ƙaramin suna ba ne a idon masu ilimi da kishin al’umma. Shi Sadauki a al’adance, shi ne gwarzo, mai jajircewa wajen kare al’ummar sa, ko da kuwa da ransa ne. Wannan laƙabi ya rataya ne a wuyan Malam Lawal Maidoki saboda irin yadda ya yi fice wajen ayyukan jin ƙai da sadaukar da rayuwarsa wajen agaza wa jama’a da rayar da al’umma ta hanyoyi daban-daban.
ɗaya daga cikin muhimman ginshiƙan da suka dasa mutuncin Malam Maidoki a zuciyar mutane shi ne, ayyukan alheri da jin kai da ya ɗora rayuwarsa a kai. Yana da cikakken imanin cewa, talakawa na da hakkin rayuwa mai inganci, kuma yana ganin sadaukarwa a gare su a matsayin nauyi, ba alfarma ba.
Wannan bawan Allah, wanda yanzu ake kira da Sadaukin Sakkwato cikin gasgatawa, mutum ne da ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimta wa al’umma. Ba tare da dora murya ba, ba tare da kafa ƙafa ba, ya zamo abin misali a tsakanin masu riƙe da amana. Bai tsaya da baki kaɗai ba, ya tsaya da aiki. Bai tsaya da alƙawari ba, ya tsaya da cikawa. Ayyukansa da halayyarsa suke magana a madadinsa.
Rikon amana da gaskiya:
A matsayinsa na Shugaban Hukumar Zakka da Waƙafi ta Jihar Sakkwato, Malam Lawal Maidoki ya taɓa dukiyar jama’a, dukiyar da wasu idan suka taɓa, sai sun yanka wa kansu alfarma. Amma shi kuwa ya yi nasarar yaƙar sinadarin kwaɗayi da ke tare da bil’adama. Ba a taɓa jin cewa an same shi da wata dambarwa ko dabarbariyar wawure kuɗi ba. Duk lokacin da aka yi ƙoƙarin ɓata masa suna, take Allah ke bayyana gaskiya, domin ciki da gaskiya, kowa ya san wuƙa ba ta isa ta yanka shi ba.
Idan akwai mutumin da bai son Malam Maidoki, to lallai ko dai shi marar gaskiya ne, ko kuwa yana da rauni a zuciyarsa. Domin ba wani mai tsoron Allah da zai soki wanda ke riƙe da amana yadda ya kamata, kuma ya sadaukar da kansa ga al’umma. Ya yi tu’amali da dubban dukiyar al’umma, ya tafiyar da su da adalci da natsuwa.
Ba ɗan siyasa ba, amma kowane ɗan siyasa na yi da shi:
Shi ba ɗan siyasa ba ne. Ba ya bin jam’iyya, ba ya da ajanda da wata maƙarkashiya ta siyasa. Amma abin mamaki, kowane ɗan siyasa na son zama da shi. Wannan kuwa saboda halayyar da ya rufe kansa na gaskiya, da rashin son kai. Duk inda gaskiya take, can ne zaka same shi. Duk inda za a raba alkhairi cikin adalci, to Malam Maidoki na ciki.
Da yana son duniya, da ya riga ya tara dukiya har ya shanye duwatsu. Amma sai ya zaɓi lahira fiye da duniya, sai ya fi son Allah fiye da lambar yabo, sai ya fifita tausayin talaka fiye da wawura.
Bakinsa ba ya cizo:
Daga cikin ababe masu ɗaukar hankali wajen kallon halayen Sadaukin Sakkwato, akwai ma’abunci zumunci ne, wanda hakan yasa mutane da dama ke da ikon zuwa gare shi don kai koke-kokensu. Bai da katanga tsakanin sa da mutane. Bai da shamaki, ba ya da fuska biyu, ba ya takama da girma.
Ko an yi masa izgilanci, sai ya kalli abu da idon hikima. Yana da ilimin mu’amalat, yana da haƙuri, yana da basira. Mutane na jin daɗin zama da shi saboda yanda yake da sauƙin kai da wuyar fushi.
Tsayin daka a kan gaskiya:
A kullum yana ƙoƙarin tabbatar da adalci, sannan yana nuna jagoranci da nutsuwa. Ba ya bari matsin lamba ya tauye masa gaskiya. Idan duk duniya sun ce dama ne, idan gaskiya tana hagu, to shi zai bi hagu. Wannan halayya ce ta magabata na ƙwarai, halayyar da ke gina al’umma da wadata da yardar Allah.
Ya kasance mutumin da akwai shi idan ana ƙirga masu kawo sauyi a cikin jama’a ba tare da tayar da ƙura ba. Ya gina tsarin raba zakka cikin tsari, ya shirya waƙafi cikin amana. Ba ya amfani da kujerarsa wajen tara abokai na siyasa, sai dai na alkhairi.
Sadauki ne a aiki ba a suna ba:
Sunansa ya zamo kirari, kirarin gaskiya da amana. Sadaukin Sakkwato, garkuwar talakawa, makamin gaskiya, ɗan ba da hannu ba tare da neman ɗaukaka ba. Ya tsaya akan tsintsiya maɗaurinki ɗaya, ya kasance dutsen da ruwa ba ya iya kawar wa, mutumin da idan ka dube shi, zaka ji cewa har yanzu akwai rago a cikin kura.
Sadaukin Sakkwato, Madogaran mabuƙata, Mai zakka da gaskiya, Wanda bai bar yatsa a tukunya ba, Garkuwan amana da mutunci, Mai rabon alkhairi ba tare da nuna bambanci ba.
Mutum mai hankali da hangen nesa:
Sadaukin Sakkwato yana cikin waɗanda suka tsare kansu daga faɗawa tarkon son rai da neman jiki ko mulki. Sau da yawa jama’a kan kwaɗaitu da samunsa a matsayin shugaba don sauyi akan irin mulkin da ake masu, haka ‘yan siyasa na ribibinsa don samun morar tagomashin da yake da shi a tsakanin al’umma, saidai Maidoki na kawar da kai daga buƙar domin amincewa da yi da cewa, taimakon jama’a ba sai kana kan kujera ba. Wannan magana tasa ta karɓu a zukatan jama’a, tana nuna irin daidaitaccen tunani da hangen nesa da ke cikin zuciyarsa.
Yana mutunta malamai, yana biyayya ga shugabanni, kuma yana girmama dattawa da uwa uba iyaye da ko abokinsu zai amsa sunansu. Yana da halin gaskiya, iya magana, da kamun kai, halayen da suka zama abin sha’awa da kwatance ga matasa.
Jajircewa a harkar addini da tarbiyya:
Wani babban ginshiƙi na rayuwarsa shi ne, taimaka wa wajen wayar da kan al’umma da faɗakarwa. Yana tallafa wa tarukan addini, yana taimaka wa malamai da makarantu na Islamiyya. A shekarun baya, an sha ganin shi a gaban taron wa’azi, yana shan gumi wajen bai wa mutane shawara da taimako a lokaci guda.
Yana daga cikin masu neman zaman lafiya da kau da rikici, inda ya kasance cikin waɗanda ake nema a lokacin da aka yi muradin shawo kan saɓani a tsakanin ƙungiyoyin addini ko na matasa.
Yabo daga masana da jama’a:
Sheikh Malam Sulaiman Jega ya taɓa cewa:
“Lawal Maidoki sadauki ne da Allah ya azurta da imani da tausayi. Idan akwai goma kamar shi, da Arewarmu ta canza.”
Haka kuma, wata shugabar mata a Unguwar Gidan Igwai ta bayyana cewa:
“Muna kiransa Uban Talakawa. Kafin mu nemi taimako, wani lokacin shi ke kawo mana. Kamar yana jin ƙunarmu ne cikin zuciyarsa.”
Misalin da ya kamata matasa su yi koyi:
A yau da duniya ke cike da mutane masu bin buƙatunsu kaɗai, Malam Lawal Maidoki ya zamo wani ginshiƙi mai ƙarfi da ke nuna yadda rayuwa ta fi ma’ana idan aka sadaukar da ita don cigaban wasu. Ba wai kawai yana taimakawa ba ne, yana rayuwa ne domin sauran mutane.
Ya kamata matasa su ɗauki irin wannan kwatanci domin su zama jagorori, masu amfanar al’umma, ba masu cin gajiyar ta ba. Sadaukin Sakkwato ba wai yana da dukiya fiye da kowa ba ne, amma yana da zuciya da kowa ke nema, zuciyar taimako da tausayi.
Me ya rage ban da yabo?
A wannan zamanin da mutane ke auna mutum da kuɗi ko ɗaurin gindi, akwai buƙatar a koma ana auna mutum da amana, da sadaukarwa, da taimakon jama’a. Wannan ne dalilin da ya sa Malam Lawal Maidoki ya fi dacewa da yabo. Ya fi dacewa da karramawa. Ya fi dacewa da a ɗauki halayensa a mayar da su darasi.
Yana rayuwar da mutane da yawa ke girmama shi da zuciya, ba da bakin magana ba. Wannan shi ne mutunci. Wannan shi ne kwarjini. Wannan shi ne matsayin da ba a siye da kuɗi, amma ake samu da gaskiya.Ina fatan al’umma za su ci gaba da girmama irinsu Malam Maidoki, domin su ne hasken da mu ke buƙata a zamanin nan.
