Kisan matafiya a Jihar Filato abu ne mai dogon tarihi, domin ba a iya lissafi.
Dubi yadda a zamanin mulkin tsohon Gwamna Siman Bako Lalon wasu matafiya masu dawowa daga maulidi suka haɗu da tarkon mugaye. Haka a dai zamanin shi gwamna Lalon aka samu wasu waɗanda su ka tare hanya suka halaka babban soja, Janar Idris Alkali.
A kuma wannan lokaci da sabuwar gwamnatin Kaleɓ Mutwan aka samu waɗanda suka tare matafiya a hanyar zuwa ɗaurin aure.
A yanzu batun da ake ciki ni a tawa ’yar fahimtar duk rashin hukunta waɗanda suka aikata makamancin haka a baya ne har abun ya kai inda ya kai a yau. Kuma ya dace mahukumta su miƙe tsaye a daina yin tofin alatsine kaɗai, duk waɗanda ake samu da laifi, su girbin abin da suka shuka. Ta hakan ne kawai za a yi wa tufkai hanci.
Allah tsare mu daga bin son zukata da aikata munanan ayukka a dukkanin hali.
Daga Mukhtar Ibrahim Saulawa Katsina. 07066434519 / 08080140820
