Tare da CHIROMA AMINU ASID
‘Urinary Tract Infection’, wato UTI a taƙaice, wata cuta ce dake kama mafitsara, musamman ta mata. A mafi yawancin lokuta, cutar ‘bacteria’ (kamar E. Coli) ce ke haddasa ta. Cutar na iya kama kowane ɓangare na tsarin fitsari, wanda ya haɗa da:
Mafitsara (bladder) – ana kiran sa ‘cystitis’.
Tashar fitsari (urethra) – ana kiran sa ‘urethritis’.
Idan ya haura zuwa ga ƙoda (kidney) – ana kiran sa ‘pyelonephritis’, wanda ya fi hatsari.
Ta wacce hanya za ki iya gane ƙin kamu da ‘Urinary Track Infection’ (UTI)?
1. Jin zafi ko ƙaiƙayi yayin yin fitsari.
2. Yin fitsari sau da yawa, amma kaɗan-kaɗan.
3. Jin fitsari a Koda wane lokaci.
4. Fitsari mai wari ko launi mai duhu.
5. Jin ciwo ko nauyi a ƙasan ciki.
6. Jini a cikin fitsari (wani lokaci).
7. Idan ya haura zuwa koda: zazzabi, jiri, ciwon kugu mai tsanani.
Me ya sa mata suke fin samun UTI?
1. Tashar fitsari ta mata gajera ce fiye da ta maza, don haka ƙwayoyin cutar bacteria suna da sauƙin shiga.
2. Jima’i na iya kawo ‘bacteria’ zuwa mafitsara.
3. Canjin ‘hormone’ bayan haihuwa ko ‘menopause’.
4. Rashin tsaftace gabanki yadda ya kamata.
Ta wace hanya za ki magance wannan cutar?
1. Ana magance ‘UTI’ da maganin ‘antibiotics’ (maganin kashe ƙwayoyin cuta).
2. Ana shan ruwa da yawa don taimaka wa wanke mafitsara.
3. A guji jinkirta fitsari idan ana jin buƙata.
4. A tsaftace daga gaba zuwa baya bayan amfani da bayan gida.
5. A guji amfani da sabulai masu ƙamshi a cikin farji ko wurin wanka.
6. Yin fitsari bayan jima’i yana rage haɗarin cutar UTI.
Idan ba a kula da UTI ba…
Tana iya haurawa zuwa ƙoda (kidneys) kuma ta zama cuta mai hatsari.
Zai iya yawaita kuma ya koma ciwon da ke dawowa (recurrent UTI).
Tana iya shafar lafiyar haihuwa a wasu lokuta.
