Ɗan mai gida ya ɗirka wa ’ya’yan ’yan haya uku ciki

Spread the love

Ɗan wani mai gida a Nijeriya ya gudu daga gidan mahaifinsa bayan ya yi wa ‘ya’yan wasu ‘yan haya guda uku ciki – ba tare wata ta san yana tarayya da wata ba.

An bayyana hakan a cikin wani faifan bidiyo na TikTok, inda saurayin, wanda ya zaɓi a sakaya sunansa, ya ba da labarinsa yayin wata hira.

A cewarsa, yana soyayya da ’yan matan uku ne a lokaci guda kuma ya sadu da kowannen su cikin ƙanƙanin lokaci.

Ya ce, daga ƙarshe su ukun sun samu juna biyu, amma wadda ta san na wata. Da gaskiya ta fara bayyana, ya bar gida ya nemi mafaka a wurin abokinsa.

Lokacin da aka tambaye shi yadda ya yi nasarar ɓoye dangantakar a tsakanin su, ya ce ya yo komai cikin sirri ne kuma bai taɓa barin ɗaya daga cikin ‘yan matan ta yi zargin yana soyayya da wata ba.

Yayin da faifan bidiyon ke tafiya ta yanar gizo, ya jawo cece-ku-ce, inda da yawa daga cikin masu amfani da shafukan sada zumunta suka shiga sashen sharhi don bayyana kaɗuwar su, ɓacin rai, da damuwa kan lamarin.

By ukarofi