Yaran shago ya wawuri kuɗin mai gidansa ya saya wa budurwarsa wayoyi

Spread the love

Wani yaran shago ya shiga hannu bayan ya sace wa mai gidansa kuɗaɗe ya saya wa budurwarsa wayoyi huɗu da kuɗin su ya kai Naira Miliyan 1.2.

Wani faifan bidiyo ya nuna lokacin da mai gidan nasa mai suna Boss yake yi masa tambayoyi, inda aka ga yaron yana roƙon gafara yayin da budurwar ke riƙe da wayoyi huɗu.

Bayanan da aka tattara sun nuna cewa yaron ya shafe shekaru bakwai yana aiki kafin ya yanke shawarar yi wa mai gidan sa sata.

By ukarofi