Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Bunguɗu da Maru Hon. Abdulmalik Zubairu ya ɗauki nauyin ɗalibai 62 da suka yi karatu a fannonin kiwon lafiya daban-daban kuma har yanzu ba su da aikin yi da jari don fara sayar da magunguna a ƙauyukan su a faɗin mazaɓar sa.
Ofishinsa ne ya ƙaddamar da aikin tare da haɗin gwiwar kwamitin kula da ci gaban al’umma da ƙarfafa wa (SCOCODE) a yau Talata.
An bai wa waɗanda suka ci gajiyar tallafin horarwa (Orientation training) kan yadda za su tafiyar da siyar da magungunan yadda ya kamata a ƙarƙashin Hon. Zannan Bunguɗu Lafiya Jari Project Initiative.
Da yake jawabi a lokacin miƙa magunguna iri-iri ga waɗanda suka amfana, Hon. Abdulmalik wanda ya samu wakilcin tsohon kwamishinan yaɗa labarai na Jihar Zamfara Alh. Umar Jibo Bukkuyum ya bayyana cewa an zaɓo waɗanda suka ci gajiyar shirin ne daga mazaɓu 21 a mazaɓar tarayya ta Bunguɗu da Maru.
A cewarsa, Hon Abdulmalik Zubairu ya kashe sama da Naira miliyan 60 domin shirin.
“Dukkanin waɗanda suka ci gajiyar tallafin an basu shaguna da kuma magunguna na sama da Naira miliyan daya kowannensu domin fara sana’arsu a garuruwan su”.
Alh. Umar Jibo ya yabawa Hon. Abdulmalik Zubairu a kan wannan shiri, yana mai cewa shirin zai taimaka wa waɗanda suka ci gajiyar shirin domin dogaro da kansu.
Ya buƙaci waɗanda suka ci gajiyar shirin da su yi amfani da abin da aka ba su ta hanyar da ta dace don bai wa wasu damar amfana.
