
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rahotanni sun bayyana cewa sanannen jagoran ƴan bindiga, Bello Turji ya miƙa wasu daga cikin makamansa tare da sako wasu mutane guda 32 da aka yi garkuwa da su a matsayin wani ɓangare na shirin sulhu da malamai a Jihar Zamfara suka samar.
Malam Musa Yusuf, wanda ya shahara da Asadus-Sunnah, ya bayyana hakan yayin wani majalisin karatu a Kaduna, ranar Litinin.
Malamin ya ce, Bello Turji ya kuma miƙa wasu daga cikin makamansa bayan wata ganawa a Ƙaramar Hukumar Shinkafi da ke Jihar Zamfara.
Asadus-Sunnah ya bayyana cewa, al’ummar Shinkafi da tawagarsa ta malamai, sun roƙi Turji da ya bar manoma su riƙa zuwa gonakinsu da ke dazuka domin gudanar da harkokinsu cikin lumana.
Ya ce, sau uku suna zaman akan batun a watan Yuli a wani yanki na dajin Fakai da ke jihar.
“Mun gana da Turji, Ɗan Bakkolo, Black, Kanawa da Malam Ila. Jita-jitar an kashe Ɗan Bakkolo ba gaskiya ba ne.”
Malamin ya cigaba da cewa, “waɗannan mutanen su ke da alhakin rashin tsaro a yankin, kuma dukkan su sun amince da tayin zaman lafiya.”
Har’ilayau, ya bayyana cewa ƴan bindigan sun miƙa wasu daga cikin makaman nasu ne a wurare uku, sannan sun amince su bar mazauna yankin su koma aiki a gonakinsu da a baya suka karɓe iko da su.
Ya ƙara da cewa, malamai suna cigaba da tattaunawar sulhu da Turji domin sako ƙarin wasu da aka yi garkuwa da su.
Kazalika, Sheikh Musa Yusuf ya jinjina wa Shugaba Bola Tinubu da mai ba shi Shawara kan Harkar Tsaro (NSA), Nuhu Ribaɗu da Gwama Dauda Lawal na Zamfara da kuma Sanata Shehu Buba bisa goyon bayansu ga ɗaukar matakin sulhu wajen magance matsalolin ayyukan ta’addanci a yankin.
