Ruftawar bango: Mutane shida suka rasu a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

An wayi gari da kaɗuwa da samun labarin ruftawar wani bango a gidan wani magidanci mai suna Muhammad Sani Garba Dankama inda mutum shida suka rasa ran su wasu kuma suna asibiti.

Bayan ɗaukewar ruwan sama bango ya faɗawa wata uwa da ‘ya ‘yan ta guda biyar inda nan take mutane shida suka riga mu gidan gaskiya.

Kamar yadda mahaifin yaran Muhammad Sani Garba Dankama ya tabbatarwa da manema labarai cewa bayan an kammala ruwan sama da misalin ƙarfe 2:00am al’amari ya faru a unguwar Ƙofar Yamma cikin garin Dankama da ke ƙaramar hukumar Kaita ta jihar Katsina.

Muhammad Sani ya ƙara da cewa, shi bayan gidan lokacin da al’amari ya faru, inda ya ƙara da cewa lokacin da ya ji labarin bai san inda kan shi ya ke ba.

“Wannan al’amari ya rutsa da kusan mutum 10 amma dai mutum shida Allah ya yi wa rasuwa bayan faruwar lamarin, yanzu haka mutune uku suna asibiti suna karɓar magani” inji shi

A cewar sa, daga cikin waɗanda Allah ya yi wa rasuwa akwai mahaifiyar yaran Mariya Sani yar shekara 45 da kuma Mujahid Sani ɗan shekaru 20 sai Zahariya Sani yar shekara 18.

Sauran sun haɗa da Hauwa Sani yar shekara 15 dai Amira Sani yar shekara uku da kuma Nura Sani ɗan shekara 5.

Muhammad Sani Dankama ya bayyana cewa yanzu haka akwai waɗanda suka samu raunuka inda suke asibitin Katsina domin karɓar magunguna.

Mahaifin yaran ya bayyana irin kaɗuwar da ya yi lokacin da ya sami labarin faruwar wannan al’amari wanda ya ce dai ya yi wa Allah godiya, “su kuma da suka rasu Allah ya jiƙan su,”ya ce.

Yanzu haka dai yan uwa da abokan arziki na cigaba da zuwa yi wa malam Muhammadu Sani Garba Dankama ta’aziyyar rasuwar iyalansa.

By ukarofi