
Daga BELLO A. BABAJI
Wani Lakcara da ke koyarwa a wata Kwalejin ƙasar waje a Moro na Jihar Osun, Dakta Nsikak Akpan, ya fara gudanar da lakcar wasan tsere na sa’o’i 150.
Akpan yana yin hakan ne a wani yunƙuri na kafa tarihi don shiga kundin tarihi na kamfanin Guinness na wanda ya fito kowane mutum a duniya ɗaukar mafi tsawon lokaci ya na gudanar da lakca.
Blueprint ta ruwaito cewa, an fara lakcar ne a safiyar ranar Litinin, 23 ga watan Satumba, 2024 a wani ɗakin taro na kwalejin da ke birnin Moro.
Zuwa lokacin haɗa rahoton, Akpan ya ɗauki sa’o’i bakwai ya na gabatar da lakcar.
Akpan ya sanya wa maudu’in lakcar suna ‘Relationship between Men’s Environment and Health’.
Sannan, ana gabatar da ita ne a inda ake haska ta kai-tsaye saboda tantancewa.
