Gwamnatin Jihar Borno ta tabbatar da kamuwar cutar kwalera a wasu mutum biyu a cikin ɗaya daga cikin sansanin waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa.
Farfesa Baba Malam Gana kwaminshinan lafiya ne ya sanar da haka a kokacin da yake ƙaddamar da shirin rigakafin kyanda Maiduguri.
Ya cigaba da cewa, da wannan ambaliyar mun samu mutum huɗu da ake zargi da cutar da kwalera amma bayan gwaje-gwaje daga babban ɗakin gwaji na hukumar yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa (NCDC), an tabbatar da guda biyu tabbas kwalera ke damun su.
Ya ƙara tabbatar da cewa wasu gwaji na mutum huɗu an sake turawa wanda shima ana jiran sakamako.
Daga ƙarshe ya roƙi mutane da su bada haɗin kai domin ganin an daƙile duk wata annoba da ka iya tasowa a sanadiyar ambaliyar da ta auku.
