Nasarar kowanne shugaba ita ce ɗaukar shawara, musamman a tsari na dimukraɗiyya, domin mulki ne na jama’a, domin jama’a, wanda jama’a ne suke yanke shawara yadda suke ganin wannan ita ce mafita a ƙasa, kuma ita ce Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya ɗauka ta fallasa ɓarayin gwamnati. Wannan ƙudiri da yake shirin gabatar da shiga majalasun tarayya ya yi daidai, amma sai an yi taka-tsantsan kuma na hangen nesa.
ɓarayin gwamnati suna da yawa; akwai ɓarayin zaune, akwai kuma ɓarayin na zaune, amma masu lasisi, wato da ake kira ‘consultants,’ da manyansu da ƙananansu. Manyan sun haɗa tun daga bankunan cikin gida da na yankuna, kamar ADB, IMF da kuma babbansu, Bankin Duniya (WB). Mun kira su ɓarayin zaune masu lasisi ne, domin idan suka ba ka bashi, za su ɗauki ruwa, kuma za ka biya kuɗin shawarwari ‘consultancy serɓice’ har na kashi 30 cikin 100 na yawan kuɗin da aka ba ka, kuma su za ka fara biya katin bashin da ruwan da aka ɗora maka.
Wannan mene ne bambancinsa da sata? Saboda haka duk lokacin da za mu je karɓar bashinsu, sai a gaya wa ’yan ƙasa cewa, waɗannan bankuna da hukumomi ga kuɗaɗan da suka karɓa. Saboda haka sai ’yan ƙasa su san irin zaman da za su yi da su. Wanda daga ƙarshen ’yan ƙasa su za su yi wa bore da zanga-zanga ta ƙin jinin karɓar bashinsu, mu tsaya daidai buƙatunmu. Wannan yanayi ma na nuni da cewa sannu a hankali duniya za ta yi wa waɗannan bankuna da hukumomi bara’a.
Yaya za a yi da ɓarayin biro, wato alƙalami, sata ta amfani da dokoki da tsare-tsare na tafiye-tafiye ta ganin ayyuka daga wannan jiha zuwa waccan duk da cewa kowacce ma’aikata na da ofis a sakateriya tarayya, amma abin mamaki idan za a yi lissafi za ka tarar da kuɗaɗen da aka kashe na dubo aiki daga Abuja zuwa Kano ko Maiduguri ko Sokoto kai koma Fatakwal ko Legas, wato ya ninka kuɗin aikin ko kuma su yi kunnen doki.
Akwai wata satar da jihohi suka fito da ita ta bayar da kwangila ga kamfanonin waje da sunan ƙwarewa, inda za ka ji ana fitar da kuɗaɗe malala gashin tinkiya, wato biliyoyi ko tiriliyoyin nairori na gina mahaɗar titinan sama da suke kira ‘flyoɓer’ da ‘under-pass’. Maganar gaskiya magana ce ta cuwa-cuwa.
Labari ya iso mana cewa, gwamnoni nan suna yin aringizo wajen bayar da wannan kwangila sannan a ware musu kashi 30 cinkin ɗari, a fitar musu da shi da sunan za a sayo kayan aiki.
Yaya matashin waɗannan ɓarayin idan ta tashi aka tabbatar da an aikata wannan sata, fallasawa za a yi ko horo mai tsanani za a yi musu?
Mun taɓa faɗa a wannan fili cewa, “Ihu ɓarawo! Iho ɓarawo!! Ba ta hana shi sata,” amma idan aka kama shi a hukunta shi, hukunci mai tsanani, ta hanyar yi masa lamba, ta cire masa hannaye idan kuɗaɗen sun kai adadi kaza, idan kuma sun kai adadi kaza sai a yanke masa ƙafafuwa, ka ga daga nan sai dai ya koma ma’aikatar wasanni ta ƙasa ya riƙa wakiltar Nijeriya a gasar Olympic na mutane masu buƙata ta musamman, shigen wanda yake faruwa a ƙasar Faransa.
Wajen wasan sunansa ɓarawo, sai kowa shiga yin taka-tsantsan da shi, domin kuwa idan ka kai shi gidan gyaran hali, an kai shi mafakar da zai ci gaba da koya wa wasu. Idan kuma ka yanke masa hukuncin rataya ka ƙara wa Borno dawaki, domin kuwa masu wannan hali ba su yi imani da ranr lahira ba, a wajansu mutuwa hutu ce.
EFCC da ICPC da sauran hukumomi na tsaro da masu sanya ido suna tasu kururuwar ta fallasawa, amma ba ta sake zani ba, domin ɓarayin nan rayuwarsu rayuwa ce ta ɓeraye da gafiyoyi da ƙananan marasa kunya. Misali; rasa kunya ɓeran tanka da ɓerayen msallaci da ɓerayen zamani da ake kiran su da ɓeran dimka. Kowanne idan za ka ɗauki halinsa, za ka ga sun yi daidai da halayen wasu ’yan Nijeriya.
Waɗannan sace-sace ba yau ko jiya ko kuma shekaranjiya aka fara ba, an fara tun lokacin da aka yi wa Arewa da Kudancin ƙasan nan auren zobe kuma sai an raba su da gaskiya da amana, wacce aka samu mutunen Arewa da ita. Aka koyar da su babu abin bautawa illa kuɗi ko ta yaya, kai dai kada ka yarda a kama ka da laifin almundahana. Wannan shi ya ba wa ’yan ƙasa damar wawason dukiyar ƙasa.
Idan za mu iya tunawa, tun daga lokacin da aka fara koya wa sarakuna karɓar cin hanci a shekara ta 1861 lokacin da mataimakin jakadan Ingila a Legas, Mr. Mckoskry, ya roki Ingila ta ba shi dama a riƙa ba wa sarakuna ɗan abin masarufi. Haka aka yi kuwa; daga nan aka shawo kan Sarkin Legas har ya miƙa Legas ga Mckosky. Daga nan aka naɗa wa Legas gwamna, Henry Standhope Freeman, kuma aka kafa tutar Ingila. Wannan ya kawo kafuwar sabuwar dangantaka da Ingila, jiragen ruwa suka yi ta zuwa gaɓar teku. Hakan ne ya ƙara wa Ingila ƙarfin gwiwar mamaye ƙasashen Yarabawa da Delta.
Daga nan aka shiga yaɗa cin hanci da rashawa da sunan kasuwanci. A 1878 akwai manya-manyan kamfanoni guda huɗu da suke yin kasuwanci a yankin Neja, su ne Aleɗander Niller Brothers and Co daga Glasgow da James Pinnock and Co. daga Liɓerpool da West African Company daga Manchester da kuma Central Afrrica Trading Company daga London, da sunan kasuwanci su suka shuka annobar cin hanci da rashawa a duk yankin.
Bayan wani Baturen Ingila mai suna Geaoge Dashwood Goldie Toubman ya shigo ƙasar, sai ya umarce su da su je duk kamfanonin nan huɗu, ya haɗe su suka zama kamfani ɗaya mai suna kantin Kamfanin UAC. Wannan ya faru a shekara ta 1879, amma a 1882 ya mayar da waɗannan kamfanoni aka kafa sojojin da za su murƙushe sauran sarakuna na Arewa da suka ƙi bayar da haɗin kai a yi kasuwanci da suke magana akansa.
Duk wata matsala ta rashin gaskiya da aka ƙulla ta da sunan kasuwanci ita ta haifar da mulkin mallaka bayan taron Birnin Berlin da ƙasashen Turai suka kira, domin karkasa Afrika a tsakaninsu, domin kwasar dukiya, musamman ma’adanai da kayan amfanin gona. Saboda haka tun daga 1885 wannan tsari ya ke tafiya har yau ɗin nan ba su daina kwasar dukiyar ba, ta kai ta kawo yanzu ƙwaƙwale na mutane masu basira suke kwasa kamar wasu dabbobi kamar yadda suke faɗa a lokacin cinikin bayi.
Saboda haka wannan tsari na fallasa ɓarayin gwamnati za a fara shine daga tushe, wato a koma baya lokacin da aka fara kwasar amfanin gona da na dabbobi har aka je ga tagulla, azurfa da kuza zuwa yau man fetur da gas da duk dangoginsu. A fallasa ɓarayin da suke fakewa da sunan kasuwanci, wato ‘business’.
