
Daga BELLO A. BABAJI
Ɗan wasan Monaco, George Ilenikhena ya kafa sabon tarihi a gasar zakarun Nahiyar Turai bayan taimaka wa kungiyarsa doke Barcelona a wasan farko na gasar.
An sako ɗan wasan ne a minti na 59 inda ya zura ƙwallo a minti na 71 wanda ya bai wa Monaco nasara da ci 2 da 1.
Hakan ya nuna ɗan wasan mai shekaru 18 shi ne mutum na biyu mai mafi ƙarancin shekaru da ya zura ƙwallo a gasar wa ƙungiyar.
Da farko dai, Barcelona ta mamaye wasan inda daga bisani Alƙalin wasa ya bai wa ɗanta, Eric Garcia jan kati a minti goma na farko.
A minti na 16 ne Monaco ta zura wa Barcelona ƙwallo wanda bayan mintina 12 ne, Yamal Jamal ya farke. A minitina ashirin na ƙasashe ne matashin ɗan wasan ya samu zura ƙwallon da ta bai wa Monaco ta ƙasar Faransa nasara.
