
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Sabon shugaban jam’iyyar PDP, Hon. Nura Amadi Kurfi ya gargaɗi jam’iyyar APC mai mulki a Jihar Katsina da ta fara tattara komatsanta daga gidan gwamanti kafin ranar zaɓen 2027.
Hon. Kurfi ya yi wannan hannunka mai sanda ne jim-kaɗan bayan amsar rantsuwar kama aiki a matsayin sabon zaɓaɓɓen shugaban PDP ɓangaren Sanata Yakubu Lado Ɗan-Marke.
An rantsar da shugaban PDP na Katsina, Muhammad Nura Amadi Kurfi tare da sauran waɗanda za su shugabanci jam’iyyar na tsawon shekaru huɗu masu zuwa
A lokacin da ya ke magana Hon. Kurfi ya yaba wa shugabancin jam’iyyar a matakin ƙasa ƙarkashin jagorancin Alhaji Umar Iliyasu Damagum wanda ya ke tafiyar da acikin mawuyacin hali.
Shugaban jam’iyyar ya kuma nuna godiyarsa ga jagoran tafiyarsu, Sanata Yakubu Lado ƊanMarke wanda ya bayyana a matsayin wanda ya jagoranci nasarar da Atiku Abubakar ya samu a zaɓen 2023 a jihar.
Ya ce, jajircewa irin ta Sanata Lado ita ce maƙasudin samun nasarar cinye zaɓen shugaban ƙasa da wasu ƴan majalisun tarayya suka a lokacin zaɓen 2023 a Katsina.
Ya ƙara da cewa, Sanata Lado shi ne mutum ɗaya da ya kasance madugun ƴan adawa wanda ya sa PDP a Katsina ta zama kwanli kura mai shiga idon masu mulki tare da tabbatar da jin dadi da walwalar mambobinta.
Sabon shugaban ya ce shugabancinsu zai mayar da hankali ne akan abubuwa guda huɗu da suka haɗa da; tabbatar da haɗin kan ƴaƴan jam’iyyar da bin doka da oda da kyautata alaƙa da tafiya tare da kowa da kuma bai wa mambobi damar su taka rawa a fagen siyasa musamman a zaɓen 2027.
Kazalika, ya yi kira ga masu-ruwa-da-tsaki na PDP a Katsina da su bada goyon bayan da ake buƙata domin samun nasarar shugabanci da kai jam’iyyar mataki na gaba.
Tunda farko, shugaban riƙon ƙwarya na PDP a Katsina, Malam Abdulkarim Musa Maƙarfi wanda ya jagoranci shirya zaɓoɓukan, ya miƙa ragamar shugabancin a hannun sabbin shugabannin.
