Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Wani ɗan Nijeriya mai suna Salisu Ahmed ɗan shekaru 66, ya zama mutum na huɗu a duniya kuma mafi tsufa da aka samu ya warke daga cutar ƙanjamau na tsawon lokaci bayan wani dashen kwayar halitta da aka yi masa.
Ya kasance yana tare da kwayar cutar sama da shekaru talatin.
Rayuwar Salisu Ahmed ta ɗauki sabon salo a lokacin da aka gano cewa yana ɗauke da cutar ƙanjamau (HIɓ) shekaru 31 da suka gabata.
A wata hira da ya yi da Doyin David, Ahmed ya bayyana cewa ciwon da ya samu ya samo asali ne daga auren farko da ya yi, lamarin da ya yi matuƙar tasiri a rayuwarsa.
Da yake tunani a kan abin da ya faru a baya, Ahmed ya ce, “Ni Salisu Ahmed, na shafe shekaru 31 ina fama da wannan cutar.
“An tabbatar da cewa kimanin kashi 85 zuwa 90 na mutanen da ke ɗauke da ƙwayar cutar HIV sun kamu da ita ne ta hanyar jima’i.”
Tafiyar rayuwar ta kasance cikin ƙyama daga mutane. Ahmed ya ba da labarin irin wariyar da ya fuskanta, ciki har da hana shi amfani da kayan aiki tare da rasa matsayinsa na koyarwa.
“An hana ni amfani da banɗakin da ke cikin harabar gidan da nake haya, an hana ni shiga banɗaki, a da ni malami ne, don haka cikin girmamawa aka ce na daina zuwa makarantar.
“Matata ta tattara komai, ciki har da yara na, sun bar ni,” inji shi.
An yi sa’a, labarin Ahmed ya juya lokacin da aka yi masa dashen kwayar halitta a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Birnin Hope da ke Amurka.
A cewar sanarwar cibiyar, Ahmed ya shiga cikin masu sa’a bayan ya warke gaba ɗaya daga cutar ƙanjamau.
