Kwastom ta fara binciken jami’anta da zargin tatsar ’yan kasuwa a Kano

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumar Kwastom ta Nijeriya, reshen Kano da Jigawa ta ce ta ƙaddamar da bincike kan wasu jami’anta da ake zargi da tilasta wa ‘yan kasuwa biyan maƙudan kuɗaɗe a kasuwar Abubakar Rimi da aka fi sani da Sabon Gari.

Binciken ya biyo bayan ƙorafin da ‘yan kasuwar suka yi na zargin wasu jami’an hukumar na karɓar kuɗi.

A cewar jami’in hulɗa da jama’a na masu shagunan Sabon Gari, kuma ƙungiyar ‘yan kasuwa ta yanar gizo, Nazifi Auwalu, ya ce kasuwancin ya yi wa mutanensu wahala, domin kuwa yadda ake tatsar dukiyar jama’a ya sanya fargaba a cikinsu.

Nazifi Auwalu ya ce ’yan kasuwa ba sa iya fitar da kayansu zuwa wasu wuraren saboda ‘harajin’ da jami’an kwastam ke tilasta su biya. 

“Muna fuskantar mawuyacin hali domin a yanzu muna cikin mawuyacin hali na jigilar kayayyaki daga wani wuri zuwa cikin jihar Kano. Yanzu mun zama kamar ɓera da kyanwa tsakaninmu da jami’an kwastam.

“Suna bin mu lungu da saƙo na jihar suna kama kaya. Ba mu yi iyaka da ƙasa ko ta ruwa ba kuma abin da muke sayarwa galibi ana saye ne a aasar nan, musamman Legas.

“Kwanan nan wasu jami’an kwastam sun kama motar mu ɗauke da turare da suka zarge mu da safarar haramtattun kayayyaki. Motar dai an kaita ofishin kwastam aka yi awon gaba da ita ba a samu komai ba.

“ɗaya daga cikin jami’in hukumar FOU ya shaida cewa sai mun biya kuɗi naira miliyan ɗaya idan ba haka ba ba za a bar motar ta fita daga ginin ba.

Shima da yake bayyana irin halin da ya shiga, wani dan kasuwa mai suna Nura Abdullahi, ya ce an karbo masa kudi har Naira miliyan uku bayan wani ciniki da ya biya Naira miliyan biyu a ofishin kwastam na Kaduna.

Wani ɗan kasuwar Sabon Gari, ya ce jami’an kwastam sun tilasta masa biyan Naira Miliyan biyu lokacin da ya kai kaya Kaduna.

A ɓangarensa, Nazifi Auwalu, kakakin ‘yan kasuwar ya ce ba a jima da kwace mota da ta ɗauko masa turare ba, kuma ba a sake ta ba sai da ya biya Naira Miliyan ɗaya.

Hukumar kwastom ta ƙasa ta bayyana cewa ta samu labarin zargin tilasta biyan cin hanci da wasu jami’anta ke yi wa ‘yan kasuwa a Kano.

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar shiyyar Kano da Jigawa, Nura Abdullahi ya ce tuni aka fara binciken zargin, kuma za a hukunta duk wanda aka kama da laifi.

A baya an bayyana yadda wani jami’in kwastam ya gamu da ƙarshensa lokacin da ya ke bakin aiki a hannun ɗan fasa kwaurin da ake ƙoƙarin kama wa a Jigawa.

Mutumin da ake zargin ɗan fasa kwauri ne ya bankaɗe IC Hamza Abdullahi Elenwo da motarsa a ranar Juma’a, a ƙoƙarin tsere wa kar jami’an kwastom su kama shi.

By ukarofi