Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Wani Insfektan ’yan sanda ya caka wa mutum wuƙa har lahira kan cin hancin Naira 200 a garin Damaturu, fadar Jihar Yobe.
Ana zargin dan sandan da hallaka wani wanda ake zargin dillalin ƙwayoyi ne saboda ya ƙi ba shi cin hancin Naira 200 da ya nema.
Lamarin ya faru ne a Unguwar CMC, Zango, Damaturu, inda sufeto Mohammed Bulama, da marigayin suka fafata ranar Lahadi da ƙarfe 5:05 na yamma.
Wata majiya ta ce “Sufeto Mohammed Bulama ya buƙaci N200 daga hannun mamacin.
“Da mamcin ya ki amincewa, sai Insifeto Bulama ya kai masa hari da wuƙa, inda ya yanke masa wuya da ƙirji har ya kai ga mutuwarsa.”
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin ’yan sandan Jihar Yobe, DSP Dungus Abdulkarim, ya ce kwamishinan rundunar, Garba Ahmed ya bayar da umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa kan lamarin.
Da yake ƙarin haske game da lamarin, jami’in ya ce taƙaddamar kan wani ciniki “ya rikide zuwa fada, lamarin da ya sa Bulama ya daba wa Dauda wuƙa a ƙirji, shi ma Bulama ya samu rauni a kai.
“Ba tare da ɓata lokaci ba an kama wanda ake zargin a hedikwatar ’yan sanda ta ‘C’ Dibision inda ya nemi mafaka.
“Sashen binciken manyan laifuka (CID) ta fara gudanar da bincike kuma a halin yanzu Bulama yana tsare a hannun har sai an gurfanar da shi a gaban kotu,” inji shi.
