An ceto yara 19 da aka yi safarar su daga Kebbi zuwa Kuros Riba

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin jihar Kebbi da ke Arewacin Nijeriya ta ce ta yi farin ciki da nasarar da aka samu ta ceto wasu yara 19, ‘yan asalin jihar da masu fasaƙaurin mutane suka sace suka kai su Kuros  Riba da ke Kudancin ƙasar.

Gwamnan jihar Kwamred Nasir Idris ne ya bayyana haka yayin bikin karɓar yaran da aka yi a gidan gwamnatin jihar da ke Birnin Kebbi, tare da shan alwashin ƙin amince wa da irin wannan al’ada ta safarar mutane a jiharsa.

A cewar gwamna Nasir Idris, an samu nasarar ƙwato yaran ne da haɗin gwiwar hukumar NAPTIP mai hana fasaƙaurin mutane.

Ya ce yaran waɗanda adadinsu ya kai 19 dukkansu babu wanda ya wuce shekara 11.

Gwamnan ya ƙara da cewa hukumar NAPTIP ta bibiya labarin sannan ta sanar da gwamnati inda kuma suka yi tattaki zuwa birnin Calabar tare da gano yaran da wanda ake zargi da jagorancin safarar yara a jihar.

“Abin baƙin ciki, bincike da hukumar lafiya ta yi a asibiti ya nuna cewa ana kwana da ƙananan yaran ‘yan shekara 10 zuwa ƙasa, wannan ba al’adar mu ba ce,” inji Gwamna Nasir Idris.

Gwamnan Nasir Idris ya ci gaba da cewa iyaye da dama na sakaci suna ba da yaransu da sunan za a kai su makaranta, sai dai saɓanin haka ne ke faruwa da yaran.

Ya kuma ce kowanne mahaifi ya sani abin tambaya ne ga kiwon ‘ya’yansa da Ubangiji ya bashi a matsayin kyauta.

Nijeriya na daga cikin ƙasashen da ke fama da masu fasaƙaurin mutane na cikin gida da kuma na ƙetare.

Ko a ƙarshen makon jiya sai da hukumar NAPTIP ta miƙa wasu ‘yan mata takwas ‘yan Nijeriya da aka yi fasaƙaurinsu zuwa ƙasar Ghana ga iyayensu.

By ukarofi