Za mu riƙa wayar da kan mutane domin sanin ayyukan hukumar ICPC – Hon. Yusuf Ata

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Sabon shugaban Hukumar Karɓar ƙorafe-ƙorafe na ƙasa reshen jihar Kano, Rt. Hon. Yusuf Abdullahi Atah ya bayyana cewa ya fahimci cewa al’umma ma basu ma san da hukumar wacce   Gwamnatin Tarayya ta kafa ta tun a 1975 ba.

Ya bayyana hakan ne da yake zantawa da ‘yan jarida a lokacin da aka raka shi ya kama aiki a ofishin hukumar dake cikin ginin sakatariyar Gwamnatin Tarayya dake kan titin Katsina.

Ya ce ba wani tsari na wayar da kan mutane na cewa akwai hukumar idan ba za ka iya zuwa kotu ba za ka iya kawo musu ƙorafi ko da kotu ce ta yi hukunci da baka gamsu da yadda alƙali ya yi hukunci ba zaka iya kawo ƙorafi  a duba tsarin da kotu ta bi ta yi hukuncin.

Hukumar na da dama ta bibiyi tsarin in akwai kuskure zai sanar da kotu ta sake duba abinda aka yi a gyara. Akwai buƙatar a sanar da al’ummar jihar Kano su san da hukumar duk wanda yake da ƙorafi a Gwamnatin Tarayya kona jiha ko ƙaramar hukuma ko a wani kamfani ko tsakaninsa  da wani yana da dama ya zo ya kawo ƙorafi.

Ya yi nuni da cewa ƙarfin hukumar ma ya so ya zarta ma na EFCC da ICPC domin su suna yin abu ne idan an rubuto ƙorafi amma a wannan Hukumar Kwamishina yakan iya yin bincike ba sai an kawo ƙorafi ba idan ya ji ana nema a zalunci wani.

Ya ce wuri ne mai muhimmanci da aka yi shi da kyakkyawar niyyar da za a taimakawa mutane. Don haka za su haɗa kai da kafafen yaɗa labarai rediyo da talabijin da jaridu don a riƙa sanar da mutane aikin hukumar.

Ya ce ta haka ne mutane su san waje ne na amso haƙƙin mutane ba tare da nuna  bambancin jam’iya ba kowane ɗan ƙasa yana da dama ya kawo ƙorafi ko a ina mutum yake. Za su yi iya ƙoƙarin wajen sauke haƙƙi da aka ɗora masa.

RT Hon. Yusuf Abdullahi Ata ya kuma gode wa ilahirin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC tun daga kan shugaban ƙasa da mataimakinsa da shugabannin majalisun Dattawa da na wakilai da mataimakin shugaban majalisar Dattawa Barau I Jibrin da shugaban jam’iyyar na ƙasa Dakta Abdullahi Umar Ganduje bisa dama da suka bayar aka naɗa shi a kan matsayin.

By ukarofi