Mun janye tuhumar halasta kuɗin haram kan Bobrisky a bisa doka – EFCC

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wata mai gabatar da ƙara a hukumar yaƙi da masu yi wa arzikin ƙasa zagon ƙasa a Nijeriya, Bilkisu Bala ta shaida wa kwamitin majalisar wakilan ƙasar da ke bincike kan zarge-zargen cin hanci da ake yi wa wasu jami’an hukumar da na hukumar kula da gidajen gyaran hali cewa an janye tuhume-tuhumen halasta kuɗin haram da ake yi wa Bobrisky da aka fi sani da Idris Okuneye bisa doka.

EFCC ta bayyana haka ne cikin sanarwar da ta wallafa a shafinta na X.

Bilkisu Bala ta shaida wa kwamitin cewa an janye tuhume-tuhumen la’akari da bayanan wani sashen hukumar na musamman da ke yaƙi da halasta kuɗin haram da ya ce kamfanin Okuneye mai suna Bob Eɗpress ba kamfani bane na hada-hadar kuɗi ko na kasuwanci don haka ba za a iya hukunta shi a matsayin wanda ya saɓa wa dokar halasta kuɗin haram ta 2022.

Tun farko mun tuhume shi da laifuka shida kan cin mutuncin takardar naira da kuma halasta kuɗin haram la’akari da jawabin da ya yi cewa kamfaninsa Bob Eɗpress ba shi da rajista da sashen na musamman da ke yaƙi kan halasta kuɗin haram sannan kuma ba ya samar masa da wata riba.

Mai gabatar da ƙarar ta yi fatali da iƙirarin cewa janye tuhume-tuhumen na da nasaba da zargin bayar da cin hanci abin da ta ce bai faru ba.

Bilkisu Bala, wadda ta bayyana gaban kwamitin majalisar wakilan bisa rakiyar wasu manyan jami’an EFCC ta buƙaci kwamitin da ya sake yin nazari kan batutuwan da EFcc ta yi sannan kuma ya gabatar wa jama’a sakamakon bincikensa domin tabbatar da adalci.

By ukarofi