Ɗan uwan Malami ya samu muƙami jim-kaɗan bayan shigarsa APC a Kebbi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ƙasa da sa’o’i 24 da shigarsa jam’iyyar APC da ayyana goyon bayansa ga Gwamna Nasir Idris na Jihar Kebbi, Almustapha Malami ya samu muƙamin Janar Manaja na Cibiyar Sadarwar Muhalli ta jihar (KEBGIS).

Almustapha ƙani ne ga tsohon Antoni Janar na Ƙasa kuma Ministan Shari’a, wato Abubakar Malami (SAN).

Shugaban ma’aikatan jihar Kebbi, Malami Shekare ne ya sanar da naɗin muƙamin a wata takarda, ranar Talata.

Ya kuma taya shi murnar samun sabon muƙamin inda ya yi kira a gare shi da ya yi ƙoƙarin sauke nauyin da aka ɗora masa bisa ƙwarewa da kiyaye gaskiya da adalci musamman bisa la’akari da kyawawan manufofin gwamnatin jihar.

A cewar takardar, naɗin Malami zai fara aiki ne a nan take.

Ana ganin wannan naɗi a matsayin siyasa musamman ganin yadda al’umma suke ta yin cecekuce a kai yayin da wasu ke ganin hakan a matsayin lada na shiga jam’iyya mai mulki.

By Babaji