
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
An samu rahotannin da ke cewa gidajen man Kamfanin MRS a Legas sun fara sayer da kowace litar fetur akan N739, lamarin da ya janyo layukan ababen hawa masu tsawo domin amfana da rangwamen da aka samu.
A cewar jaridar PUNCH an fara sayar da fetur akan N739 a Alapere, wanda hakan ya sa kamfani ya yi wa sauran gidajen mai fintinkau.
An gano cewa wasu gidajensu mai a yankin hanyar Legas zuwa Ibadan da ke Jihar Ogun suna cigaba da sayarwa akan N875 zuwa daren Talata wayewar Laraba.
Bayan ragin da aka samu daga N828 zuwa N699 a ranar Juma’a, Shugaban rukunin kamfanonin Ɗangote, Alhaji Aliko Ɗangote ya yi alƙawarin sayarwa a famfunan mai akan N739.
