
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Talata Majalisar Wakilai ta yanke shawarar ganawa da manyan jami’an Ma’aikatun Tsaro da na Harkokin Waje bisa tsare jirgin Nijeriya a Burkina Faso.
Rahotanni sun bayyana cewa an cimma matsayar ne a ƙarƙashin ƙudirin da Ɗan majalisa daga Ekiti. Mista Rufus Ojuawo ya gabatar na buƙatar al’umma ta gaggawa.
Yan majalisar sun yi kira ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da ta yi amfani da tsare-tsaren ƙungiyoyin ECOWAS da AU wajen samar da haɗin kai da fahimtar juna da za su taimaka wajen sako jirgin sojojin da kuka jami’an sojojin da aka tsare a ƙasar.
Sun kuma yi kira ga ofishin mai ba Shugaban Ƙasa Shawara akan Harkar Tsaro (ONSA) da ya samar da tsarin tattaunawa wajen ganin an warware matsalar ba tare da faɗaɗa ta ba.
Haka kuma, majalisar ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta samar da bayanai na gaskiya ga al’umma akan al’amarin domin kauce wa shiga ruɗu daga bayanai na ƙarya da ake yaɗawa, lamarin da zai taimaka wajen bada kariya ga tsarin difulomasiyya da tsaro.
A ranar 8 ga watan Disamba, 2025 ne jirgin, wanda ke ɗauke da sojoji 11 ya yi saukar gaggawa a Burkina Faso bayan ya tashi daga Legas da nufin zuwa Portugal.
