Daga SHEHU MUSTAPHA CHAJI
Yayin da muka tinkari zaɓen 2027 wasu ‘yan siyasa da suka sami damar riƙe manyan muƙamai kuma jihohin su da Arewa basu amfana da damar da suka samu ba, sune a yanzu suke yaɗa farfagandar cewa Shugaba Tinubu baya komai wajen samar da cigaba! Shugaba Tinubu ya maida Arewa saniyar ware! Da sauran kalaman farfagandar domin tunzura wasu yan Arewa kar su sake zaɓen Shugaba Tinubu.
Da mamaki a ce har wasu yan Arewa sun manta da wahalar yunwa da ƙunci da suka kwashe shekaru suna sha ƙarƙashin mulkin ɗan Arewa. A yanzu yan Najeriya suna ci su ƙoshi kan farashi mai matuƙar sauƙi. A yau mafi yawan yan Arewa sun koma gonakin su sun cigaba da noma bayan kwashe shekaru basa iya noma.
Shugaba Tinubu kuma ya ɗauki manya manya muƙamai ya danƙawa yan Arewa. A majalisar tarraya da kakakin majalisar wakilai da mataimakin shugaban majalisar dattijai da masu tsara yanda za’a kashe kuɗin Najeriya aka naɗa yan jihohin Kano da Kaduna.
Dan kawo ƙarshen rashin tsaro Shugaba Tinubu ya naɗa yan Arewa daga jihohin Kaduna da Zamfara da Adamawa da Kano da Jigawa su jagoranci samar da tsaro a Najeriya.
Ta fannin tattalin arziki ana ta samun cigaba duk da wasu yan Arewa ne ke ƙoƙarin daƙile cigaban da Aliko Ɗangote ya kawowa ƙasar mu.
Matsalar Najeriya a yanzu yan Najeriya ne matsalar ƙasar.
Duk da sauƙin farashin kayan abinci da aka samu masu sayar da dafaffen abinci sun ƙi ƙara hannu balle rage farashi. Masu Motocin haya da yan adaidaita sahu sun ƙi rage farashin ɗaukar fasinja.
Masu biredi sun ƙi rage farashi duk da sauƙi da ake samu kan farashin fulawa.
Masu bada gidajen haya kullum sai ƙara kuɗi su ke.
Kuma tun ranar da aka cire tallafin man fetur kuɗaɗen da jihohi suke samu ya ninka har sau uku ko fiye har da wasu kuɗaɗe na musamman da Shugaban Ƙasa ke turawa gwamnoni, shin akwai wani cigaba na daban da suke samarwa dan inganta rayuwar al’ummar su?
In ‘yan Arewa za su kasance masu adalci ya zama wajibi su tafawa Shugaba Tinubu saboda a ƙanƙanin lokaci rayuwar su ta canza. An daina ko an samu raguwar masu cire tafasa da rai ɗore da sauran ganyeyyaki a daji da sayen shinkafar afafata da sauran su. Mutane suna iya sayen abinci mai kyau kan farashi mai sauƙi.
Domin ɗorewar cigaba da ake samu a fannonin cigaba da bunƙasar tattalin arziki yan Najeriya musamman yan Arewa su yi tururuwa su sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a karo na biyu.
