MOPPAN da hukumar tace finafinai za su tsaftace kasuwancin fim a Yobe

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙungiyar Masu Shirya finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) reshen Jihar Yobe da haɗin gwiwar hukumar tace finafinai ta jihar za su tsaftace harkokin kasuwancin finafinan Hausa, inda suka dakatar da sayar da fostar finafinai ba tare da mallakar lasisin kamfani ba a faɗin jihar.

A wani saƙo daga shugaban MOPPAN na jihar, Khalifa Bulau, ƙungiyar ta koka game da yadda wasu ɓata-gari ke amfani da sunan masana’antar Kannywood wajen tilasta wa ƴan tura fim da aka fi sani da ‘ƴan downloading’ biyan tara ko kuma ƙwace musu lassisin yin aiki.

A cewarsa, a kan soki masana’antar kai-tsaye da sunan tana gudanar da aiki ba bisa ƙa’ida ba don haka suka ga dacewar shaida wa al’umma cewa ba su da hannu a cikin haka.

A ƙoƙarinta na samar da tsafta cikin ayyukanta, MOPPAN ta barranta kanta daga haka, tana mai gargaɗin ƴan turi da su tabbatar da cika ƙa’idojin sanarsu gabanin cigaba da gudanar da hulɗa a cikin al’umma domin kaucewa shiga matsala.

Haka kuma, ƙungiyar ta gargaɗi jami’an da ke da alhakin kamen, da su tabbatar da bin sharuɗɗan da aka gindaya musu a hukumance ta yadda za su riƙa yin aiki ba tare da tsangwama ko tauye ƴancin waɗanda abin ya shafa ba.

By Babaji