Ɗangote ya sauko daga mataki na mafi kuɗi a Afrika

Spread the love

Ɗangote ya sauko daga matakin wanda ya fi kowa kuɗi a Afirka biyo bayan Johann Rupert da ya wuce shi da jimillar kuɗi Dala biliyan 13.65.

A wani rahoto da Bloomberg su ka fitar na masu kuɗin duniya, Rupert ya kasance a mataki na 154 inda ya wuce Ɗangote da mataki biyu.

Wannan rahoton ya nuna cewa Ɗangote ya yi asarar Dala biliyan 10 a cikin watanni shida wanda ya janyo jumullar kuɗin shi su dawo Dala biliyan 13.6 inda Rupert ya wuce shi da Dala miliyan 50.

Wannan saukowa da Ɗangote yayi za a iya danganta shi irin matsin tattalin arziki da Nijeriya ke fuskanta da kuma rashin darajar Naira in a ka haɗa ta da dalar Amurka.

By ukarofi