
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
A kwanan nan ne Shugaba Tinubu zai gabatar da ƙudirin tsarin fallasa ɓarayin gwamnati ga Majalisar Ƙasa don ɗaukar mataki daga gare ta.
Ministan Kuɗi kuma ministan shirya Tattali, Wale Edun ya faɗi hakan a Abuja a lokacin wani zama da aka yi wa laƙabi da ‘Implementing the whitselblowing policy in Nigeria issues, challenges and the way forward.’
Ya ce, gwamnatin tarayya ta na buƙatar taimakon ƴan Nijeriya wajen sanya tsarin ya yi aiki ta hanyar tabbatar da gaskiya da adalci.
Edun yace tsarin fallasar na daga cikin salo da gwamnati ta ɗauka wajen tabbatar da cewa an gudanar da ofisoshin gwamnati bisa tsari.
Ya ƙara da cewa, tsarin zai taimaka wajen tabbatar da an yi adalci a tafiyar da harkokin ofishin gwamnati ta yadda ƴan ƙasa zasu ke sanya ido game da kai-kawo na kuɗaɗen ƙasa.
