
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Gwamnatin Tarayya zata ɗauki matakin cire Nijeriya daga cikin jadawalin ƙasashe masu fuskantar barazanar tattali na FATF kafin watan Mayu na shekarar 2025.
Shugaban ma’aikatan Fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila ya bada tabbacin hakan a wani ziyarar bincike da ya kai ofishin cibiyar leƙen asiri na harkar kuɗin Nijeriya, NFIU a Abuja inda ya ce gwamnatin tarayya zata yi ƙoƙarin warware matsalolin da suka sa ta kasance ɗaya daga ƙasashen jadawalin.
Gbajabiamila ya bayyana haka ne bayan da Darakta-Janar kuma shugabar NFIU, Hafsat Bakari ta nemi a gaggauta kai wa matakin da FATF ta zayyana acikin tsarinta don cire Nijeriya daga cikin masu fuskantar barazanar kuɗi.
A ranar 23 ga watan Fabrairu ne aka sanya sunan Nijeriya acikin jadawalin sakamakon koma baya da Nijeriya ta ke samu ta ɓangaren kuɗi wajen daidaita matsalar satar kuɗi, ta’addanci da sayan makamai.
FATF wata ƙungiya ce ta gwamnatoci mai zaman kan ta da ke ƙoƙarin inganta tsare-tsare don tseratar da ƙasashe daga shiga rukunin barazanar kuɗi.
Shugaban ma’aikatan ya kuma yaba wa ƙoƙarin NFIU na cimma kaso 30 na tsarin FATF da ake buƙata, ya na mai nuna muhimmancin samar da sauran kason don kai Nijeriya ga nasarar fita daga cikin jadawalin.
