2022: Buhari ya gabatar da kasafi mafi tsada a tarihi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

A jiya Alhamis ne Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya gabatar da jimillar kasafin kuɗi na Naira tiriliyan 16.39 na shekarar 2022 ga babban zauren Majalisar Tarayya, wanda shine kasafi mafi tsada da aka gabatarwa a tarihin Nijeriya.

A jawabinsa na gabatar da daftarin kasafin na Naira tiriliyan 16.39, Buhari ya shaida wa zauren majalisar cewa kasafin 2021 ya samu matsala, saboda Nijeriya ta samu durƙushewar tattalin arziki sau biyu, amma ta yi nasarar fitowa daga matsalar.

Ya ƙara da cewa, a 2021 an samu kuɗaɗen shiga daga vangaren da ba na mai, kuma sun qaru da kashi 7 cikin 100 a shekarar, amma kuma an gaza cimma hasashen kuɗaɗen shiga daga vangaren mai.

A cewarsa, annobar Korona ta yi tasiri wajen raguwar man da aka haƙo.

Idan ba a manta ba, Majalisar Tarayya ta amince da kasafin 2022 zuwa 2024, a kan farashin gangan ɗanyen mai Dala 57, savanin Dala 40 na kasafin 2021.

Kasafin ya sanya farashin Dala a kan Naira 410, haƙo gangar mai miliyan 1.88 a kowace rana a 2022, miliyan 2.23 a 203 da kuma miliyan 2.22 a 2024. Ya ce, giɓin Naira tiriliyan 5.01 da aka samu ta hanyar karɓo rance.

Ya kuma bayyana cewa, kasafin kuɗin 2022 shine karo na farko a tarihin Nijeriya, inda aka shawarci MDA a kan kasafin kuɗi mai dacewa.

“Waɗannan ɓangarori ne na muhimman matakai a ƙoƙarinmu na rarraba albarkatu daidai kuma mu isa ga ƙungiyoyin jama’a masu rauni,” inji shi.

Bayan gabatar da kasafin ne zai miƙa wa daftarin ga majalisar ta yi aikin tantance abin da ke ƙunshe a ciki gabanin amincewa da shi.

Gabanin amincewar majalisar, kwamitocinta za su bi diddigin abin da ke ƙnushe ciki ta hanyar yi wa shugabannin hukumomi da ma’aikatu da cibiyoyin gwamnati game da abin da aka ware musu a kasafin.

Jami’an tsaro sun yi wa harabar Majalisar tsinke, inda suke tsaurara bincike akan duk wanda da zai shiga ko ya fita daga harabar.