Shauƙin zama likita gado ne na gidanmu, Inji Saraki

Daga NASIR S. GWANGWAZO

Tsohon shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, kuma tsohon gwamnan Jihar Kwara, Dakta Abubakar Bukola Saraki ya bayyana dalilin da ya sa ya zama likita. 

Saraki ya yi wannan bayani ne yau a wurin taron ƙasa na Kungiyar Ɗalibai Likitoci ta Nijeriya wanda aka gudanar a Jami’ar Baze dake Abuja.

Dr. Abubakar Bukola Saraki shi ne Uban Taron na, wanda bayan buɗe taro da ya yi Kungiyar ta girmama shi da lambar yabo.

A cikin jawabinsa ya ce: “A al’adar gidanmu, mun mayar da zama likita wata kafa ta taimakawa masu buƙatar taimako. Ina ɗan shekara 12 na kamu da shauƙin zama likita – musamman ma saboda marigayi mahaifina likita ne.

“Bayan shekaru, ita ma ɗiyata tana shekara 12 ta ayyana cewa likita take son zama. Yanzu haka tana shekara na huɗu a makarantar horas da likitoci.

“Saboda haka ne a yau da na ke jawabi ga membobin ƙungiyar ɗalibai likitoci ta Nijeriya a taronsu na shekarar 2021 wanda ya gudana a Jami’ar Baze da ke Abuja, na cika da farin cikin ganin ɗalibai matasa masu hazaƙa – waɗanda suka haɗu wuri guda don shirya bahasi kan larurorin kiwon lafiya da suka shafi dukkan ‘yan Nijeriya.” Inji shi