2023: Osinbajo ya bi sahun masu kwaɗayin shugabancin Nijeriya

Daga BASHIR ISAH

Mataimakin Shugaban Nijeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, ya bayyana ƙudirinsa na neman takarar shugaban ƙasa a babban zaɓe mai zuwa.

Osibanjo ya bayyana ƙudirin nasa ne cikin wani taƙaitaccen bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Tiwita.

Wannan na zuwa ne kwanaki 89 bayan da ubangidansa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, shi ma ya bayyana aniyyarsa ta neman tsayawa takarar shugabancin ƙasa.

Sa’ilin da yake bayyana ƙudirin nasa, Osinbajo ya ce, “Tare da ƙanƙan da kai, a yau ina mai bayyana ƙudirina na neman ofishin shugaban ƙasar Tarayya Nijeriya a hukumance ƙarƙashin inuwar jam’iyyar All Progressive Congress (APC).

“Idan Allah ya yarda kuma mutane suka amince har na samu wannan damar, to ina da yaƙinin cewa abu na farko da za mu maida hankali a kai shi ne ƙarasa ayyukan da muka soma.

“A hankali za mu gyara tsarin tsaro da kuma kammala garambawul a ɓangaren shari’a. Za mu maida hankali wajen walwalar ma’aikatan shari’a domin tabbatar da an yi wa kowa adalci yadda doka ta tanada.”

Kafin wannan lokaci, ana ta raɗe-raɗin Osinbajo ma na da sha’awar mulkin Nijeriya, amma sai a wannan lokaci ya fito ya tabbatar da gaskiyar raɗe-raɗin.