2025/2026: Manchester United za ta karɓi baƙoncin Arsenal a wasannin farko na Premier League

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar kula da gasar Premeir ta ƙasar Ingila (FA) ta fitar da jaddawalin gasar na bana, wanda za a fara ranar Juma’a, 15 ga watan Agustan 2025.

Wadda ta lashe gasar a kakar da ta gabata, wato Liverpoool, za ta fara kare kambin ne a gida inda za ta haɗu da Bournemouth a ranar farko ta gasar a kakar wasa ta 2025/26.

Manchester United kuwa, za ta fara gasar ne da karawa da babbar abokiyar hamayyarta, Arsenal a filin wasa na Old Trafford.

Liverpool ta lashe gasar ne a kakar farko ta sabon kocin ƙungiyar, Arne Slot da maki 84, yayin da Arsenal ta ƙare a mataki na biyu da maki 74.

Sabuwar ƙungiyar da ta hauro gasar a bana, Sunderland za ta fara gwada ƙarfinta a gasar a gida da karawa da West Ham.

Zakarar gasar Championship kuwa, wato Leeds United, za ta fara da karɓar baƙuncin Everton a ranar Litinin a makon farko, yayin da Burnley da ita ma ta sake dawo wa gasar a bana, inda za ta ziyarci zakarun gasar Europa League Tottenham.

Mancheste City kuwa, wadda ta ƙare kakar bara ba tare da kowane kofi ba, za ta ziyarci Wolverhampton Wanderers a filin wasa na Molineux.

Za a buga wasa 380 a kakar gasar ta bana cikin mako 38, yayain da za a kammala gasar a ranar 24 ga watan Mayun 2026, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

By Babaji