Iran ta jefa makamai a na’urar tsaron Isra’ila

Spread the love

Iran ta fara ƙaddamar da hare-haren akan wasu sassan Isra’ila a wanan karon da shu’umin makami mai linzami samfurin Fattah a cikin daren Talata wayewar safiyar Laraba a yayin da Isra’ila ta mayer da martani ta hanyar kai gagarumin farmaki a wajen birnin Teheran da cibiyoyin soji da kuma wata babar jami’a.

Dakarun juyin juya hali na Iran a nasu ɓangaren, sun shaida cewa makamai masu linzamin da ƙasar ta harba sun kutsa kai ne cikin na’urar tsaron Isra’ila tare da haddasa ɓarna mai tarin yawa a wasu sassan ƙasar.

Ya zuwa yanzu ƙasashen biyu ba su fitar bayanai a game da irin ɓarna da hare-haren da suke kai wa juna ke yi musu ba.

Saidai, ƙungiyar rajin kare haƙƙin ɗan-adam (Human Rights Activists) da ke zaune a Amurka, ta ce aƙalla Iraniyawa 585 hare-haren Isra’ila suka hallaka ciki har da gomman mata da yara ƙanana, yayin da wasu mutum 1,277 suka samu raunuka.

A ɓangaren Isra’ila, ƙungiyar ta ce an kashe mutum 24 ba yaga wasu daururuwan da suka jikkata.

RFI Hausa ta ruwaito cewa, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Shugaban Amurka Donald Trump, ya buƙaci Iran ta miƙa wuya ba tare da wani sharaɗi ba, yana mai cewa suna da bayanai a game da inda jagoran addinin Jamhuriya Muslunci ta Iran AyatollAh Ali al’hamna’i ya ɓuya saidai ba su da niyyar hallaka shi.

By Babaji