Yanzu-yanzu: Shugaba Tinubu ya isa Benuwai kan kashe-kashe

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Tinubu ya isa Makurɗi, Babban Birnin Jihar Benuwai domin ziyartar mutanen Ƙauyen Yelwata dake Ƙaramar Hukumar Guma a jihar.

Tinubu ya isa Filin jiragen sama dake sansanin sojojin sama na Makurɗi ne da misalin ƙarfe 12:58 na rana.

Zai gana ne da muhimman masu-ruwa-da-tsaki a jihar da nufin kawo ƙarshen munanan hare-haren da suka yi sanadin mutuwar mutane da dama a sassan jihar.

A saboda haka ne gwamnatin jihar ta sanar da yau Laraba a matsayin ranar hutu ga ma’aikata a jihar.

By Babaji