Ƙofar sulhu da ‘yan bindiga a buɗe take – Gwamnatin Sakkwato

Spread the love

Gwamnatin Jihar Sakkwato ta bayyana shirinta na tattaunawa da ‘yan bindiga da ke da niyyar ajiye makamansu tare da komawa cikin zaman lafiya. A cewar wani jawabi daga mai baiwa gwamna Ahmed Aliyu shawara kan tsaro, Col Ahmed Usman (rtd), gwamnatin ta ce tarihi ya nuna cewa yawancin rikice-rikice ba su kare da ƙarfin bindiga kadai ba, sai da tattaunawa mai ma’ana.

Gwamnatin ta godewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da shugabannin tsaro da duka jami’an da ke bakin aiki saboda irin ƙoƙarin da suke yi wajen kare yankin. Ta yi addu’ar Allah ya jiƙan sojojin da suka rasa rayukansu, ya kuma ba iyalansu haƙurin rashi.

Dangane da shirin kafa masu gadin daji a Arewacin ƙasar nan, gwamnatin ta nuna goyon bayanta amma ta nemi a gudanar da ɗaukar ma’aikatan cikin gaskiya da amana. Haka kuma ta buƙaci a sanya su ƙarƙashin kulawar hukumomin tsaro don gujewa cin zarafi da rashin ɗa’a.

Gwamnatin ta Jihar Sakkwato ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da tallafawa duk wani shiri da ke neman kawo zaman lafiya mai ɗorewa. Ta kuma jaddada cewa babu abin da za a rage wajen tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a faɗin jihar.

By ukarofi