2027: An gayyaci Tinubu, Atiku, Obi da wasu huɗu zuwa muhawarar shugaban ƙasa a Abuja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Zaɓen shugaban ƙasa na 2027 na shirin samar da babban tsarin gudanar da muhawara, yayin da Ƙungiyar Sirrin Siyasa, wato Political Intelligence Group (PIG) ta Politico.ng, ta sanar da shirinta na karɓar baƙuncin ‘yan takarar shugaban ƙasa guda shida a ranar 10 ga Junairun 2027 a Abuja.

Rahotanni sun ce, taron muhawarar na tsawon sa’o’i uku, na da nufin bai wa masu zaɓe damar nazari kan tsare-tsaren ‘yan takara, nagartar jagoranci da matakansu na warware matsaloli da ƙalubalen da Nijeriya take fuskanta gabanin zaɓukan.

Waɗanda aka gayyata sune Shugaba Bola Ahmed Tinubu na All Progressives Congress (APC); Atiku Abubakar na African Democratic Congress (ADC); Peter Obi na Nigeria Democratic Congress (NDC); Seyi Makinde na Allied Peoples Movement (APM); Donald Duke na Peoples Redemption Party (PRP); da kuma Adewole Adebayo na Social Democratic Party (SDP).

Jagoran ƙungiyar, Lai Omotala ne ya bayyana wannan shiri a wani taron manema a Legas, ranar Juma’a, inda ya ce an samar da shirin ne da nufin ƙarfafa wa yaƙin neman zaɓe masu kyawawan manufofi da ƙarfafa tsayar da gaskiya da adalci a tsarin dimukraɗiyya.

Ya bayyana cewa, zaɓen 2027 na ɗaya daga cikin mafi fuskantar ƙalubale a tarihin Nijeriya, inda ya ce muhawarar ‘yan takarar ka iya zama ɓangare na manyan zaɓukan Nijeriya domin ƙarfafa wa ‘yan ƙasa gwiwa yayin zaɓar ‘yan takararsu musamman a matakin shugaban ƙasa.

By Babaji

Leave a Reply