
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, ya sabunta tsarin yaɗa labaransa wanda ya taƙaice wa jami’ai uku kacal su wakilce shi a ɓangaren, yayin da aka samu cece-kuce kan wasu daga cikin waɗanda aka sanar da naɗa su a matsayin kakakinsa a baya.
Rahotanni sun ce, kwamitin a wata sanarwa, ya ce an yi wannan sauyi ne da nufin tabbatar da bunƙasa tsarin gudanarwa, horo da hulɗa da jama’a bisa inganci gabanin zaɓe shugaban ƙasa na 2027.
A ƙarƙashin sabon tsarin an zaɓi Darakta-Janar na kwamitin, Sanata Abdulaziz Yari; Ministan Albarkatun Ƙasa, Dele Alake, ya zama ainihin kakaki a hukumance; da Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Alhaji Mohammed Idris, a matsayin wanda zai riƙa magana a madadin kwamitin.
Kwamitin ya umarci baƙi ɗaya mutanen da ke magana da yawunsa a baya da su koma ƙarƙashin ɓangaren yaɗa labarai da dabarun sadarwa a matsayin mambobi, wanda hakan ya rushe su kai-tsaye daga matsayin kakaki.
Haka kuma, ya shawarci kafafen yaɗa labarai da su kasance a faɗake game da sauyin, inda ya ce kwamitin zai wakilta waɗanda suka dace su wakilce shi yayin hirarrakin da suka shafi yaɗa labarai idan da buƙata.
Wannan na zuwa ne yayin da wata taƙaddama da ta haɗa Alwan Hassan, ɗaya daga cikin kakakin da kwamitin APCn ya sanar a baya ta haifar da cece-kuce, sakamakon wata hirarsa ta gidan talabijin da ya kai ga jam’iyyar ta soma ƙoƙarin kare kanta.
