
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Yayin da ake cigaba da shirye-shiryen babban zaɓe na 2027, wasu mambobin jam’iyyar PDP na Kwamitin zartarwarta (NEC) sun bayyana mabanbanta ra’ayoyi game da ko su bi dokarta na tsarin karɓa-karɓa ko kuma su tafi akan mafiya rinjaya.
Hakan faru ne a lokacin da ake ganin akwai yiwuwar tsohon shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya fice daga jam’iyyar da kuma shawarar da jigo a jam’iyyar, Olabode George ya bayar na a ɗauko ɗan takara daga kudu matuƙar ana son jam’iyyar ta yi nasara.
Jigon ya bayyana hakan ne a yayin hira da manema labarai, inda ya ce waɗanda suka kafa PDP ne suka amince da tsarin karɓa-karɓa duba da rabe-raben yaruka da shiyyoyi da ƙasar ke da su.
Akan haka ne Diran Odeyemi, wanda mamban NEC ne a jam’iyyar, ya amince da matsayar George inda ya ce hakan abu ne mai muhimmanci ga zaɓen 2027, yana mai cewa lallai hakan zai taimaka wajen cimma matsaya a babban taron jam’iyyar wanda za a yi a ƙarshen 2025.
Haka kuma, manyan ƴan jam’iyyar sun ce lallai akwai buƙatar a yi sulhu da waɗanda ke hana ruwa gudu a jam’iyyar da warware rikici tsakanin ƴaƴanta domin kai wa ga nasara, yana mai bada misali da Wike wanda ac cewarsa ake matuƙar buƙatarsa a jam’iyyar.
