Ana zargin wata mata mai suna Khadija kan kashe ’yarta mai shekaru 11, Fadila, saboda Naira 100 da ta samu a yawon Sallah a unguwar Tukur-Tukur da ke ƙaramar Hukumar Zariya a Jihar Kaduna.
Lamarin ya faru ne a ranar Asabar kafin sallar Magariba, inda lamarin ya janyo cece-kuce a unguwar har maƙwabta suka ƙi yi wa gawar yarinyar sallah saboda tsoron abin da zai biyo baya.
Wasu maƙwabta sun bayyana cewa Khadija ta doki Fadila da taɓarya ne saboda ta zargi yarinyar da satar Naira 100.
Sun ce irin wannan ɗabi’a na duka da tsangwama ba sabon abu ba ne domin sau da dama idan ta tura Fadila talla aka samu matsala, sai ta lakaɗa mata dukan tsiya.
Wani mutum ya ce: “Dalilin da ya sa muka ƙi yi mata sallah shi ne, ba a ɗauki matakin da ya dace ba. An zubar da gaskiya. Saboda haka mu ma muka yanke shawarar ba za mu yi mata sallah ba.”
Amma mahaifiyar da ake zargi, wato Khadija, ta musanta zargin cewa ta yi wa ’yarta da duka da taɓarya.
Ta ce a lokacin da ta ke dukan yarinyar, ba kowa a gidan sai yara.
Mijin matar, Malam Mustapha Musa, ya shaida cewa lokacin da lamarin ya faru ba ya gida, don haka bai san yadda abin yake ba.
Tuni mahaifin Fadila ya ɗauki gawar ’yarsa zuwa ƙauyensu da ke jihar Kano domin yi mata sutura.
Ya ce, “Na bar komai da hannun Allah.”
Wani jami’in tsaron sa-kai wanda ya buƙaci a sakaya sunansa ya ce, sun gayyaci Khadija da mijinta ofishinsu domin amsa tambayoyi, amma daga baya sai suka janye bayan sun ga ’yan sanda sun isa wajen.
