2027: Hon. Nalaraba ya janye daga takarar gwamna zuwa ta sanata

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Ɗan majalisar wakilai na tarayya dake wakilyar Nasarawa ta Kudu a jihar Nasarawa Honorabul Abubakar Hassan Nalaraba ya sanar da janyewarsa daga takarar kujerar gwamnan jihar ta Nasarawa inda yace a yanzu ya koma neman kujerar sanata ne don wakiltar mazaɓar a majalisar dattawa ta kudancin jihar Nasarawa.

Ya sanar da haka ne a lokacin wata ganawa na musamman da mambobin ƙungiyar yaƙin neman takararsa ta kujerar gwamna daga ƙananan hukumomi 13 na jihar.

A cewar Honorabul Abubakar Hassan Nalaraba ya yanke shawarar yin haka ne a matsayinsa na mai kishin ƙasa dake saka cigaban jihar a gaba a kullum da kuma yin biyayya da girmama matakin gwamnan jihar mai ci yanzu Injiniya Abdullahi Sule na zaɓin Sanata Ahmed Aliyu Wadada a matsayin wanda zai gaje shi a kujerar gwamnan a zaɓen 2027 kasancewarsa cikakken ɗan jami’ar APC kuma ya riga yayi alƙawari cewa a ƙarshe duk wanda gwamna Sule ya zaɓa cikinsu ‘yan takarar zai mara masa baya ba wai don ya karaya ko ya gaza ba ne.

Ɗan takarar ya kuma yi amfani da damar inda ya umurci ɗimbin magoya bayansa daga duka ƙananan hukumomin jihar 13 su mara wa zaɓin gwamnan wato Sanata Ahmed Aliyu Wadada baya a zaɓen don ɗorawa daga inda Abdullahi Sule zai tsaya kana sauran magoya bayan nasa daga Kudancin jihar ya buƙace su su fito ƙwansu da kwarkwata su zaɓe shi a kujerar sanatan don bashi damar cigaba da gudanar da ire-iren ayyukan cigaba da aka san shi da yi a majalisar wakilai.

Wakilinmu a jihar ya kuma ruwaito cewa daga bisani ɗan takarar gwamnan wanda ya koma neman sanatan Honorabul Abubakar Hassan Nalaraba ya kuma gana da manema labarai inda ya tabbatar musu da matakin nasa na canja takarar a hukumance.

Daganan sai ya bayyana wasu daga cikin kyawawan shirye-shirye da tsare-tsaren ayyukan cigaba da zai gudanar don amfanar al’ummarsa na mazaɓar sanatan idan Allah ya bashi nasara.

Daga bisani ɗan takarar ya kuma jagoranci ɗimbin magoya bayan nasa zuwa ofishin jami’ar APC na jihar dake nan Lafiya inda ya sayi fom na nuna sha’awarsa na neman takarar sanatan.

By ukarofi