Yadda ACReSAL ke gina ‘yan jarida kan sauyin yanayi ya ja mata karramawa a Gombe

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe

Shirin Agro-Climatic Resilience in Semi-Arid Landscapes (ACReSAL) a Jihar Gombe ya samu gagarumar karramawa daga ƙungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ), sakamakon ƙoƙarinsa na horar da ‘yan jarida kan yadda za su riƙa ba da rahotanni masu inganci kan sauyin yanayi.

An bayar da wannan lambar yabo ne a yayin bikin cin abinci da raba kyaututtuka na shekarar 2025 da NUJ ta shirya a Gombe, inda aka bayyana ACReSAL a matsayin hukuma mafi mu’amala da kafafen yaɗa labarai a jihar.

Masu shirya taron sun jaddada cewa shirin ya taka rawar gani wajen inganta fahimtar ‘yan jarida kan batutuwan sauyin yanayi, lamarin da ya taimaka wajen wayar da kan al’umma kan matsalolin muhalli da hanyoyin magance su.

Da yake karɓar lambar yabon, mai kula da shirin ACReSAL a jihar, Dokta Sani Adamu Jauro, ya bayyana cewa wannan karramawa wata shaida ce ta nasarar da aka samu wajen gina kyakkyawar alaƙa tsakanin shirin da kafafen yaɗa labarai.

Ya ce horar da ‘yan jarida na daga cikin manyan manufofin shirin, domin tabbatar da cewa ana isar da sahihan bayanai ga jama’a kan sauyin yanayi da tasirinsa ga rayuwar al’umma.

Jauro ya danganta wannan nasara da goyon bayan Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, wanda ya ce ya ba da fifiko ga haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da ‘yan jarida domin inganta sadarwa da gaskiya.

Haka kuma, ya yaba wa ‘yan jarida bisa rawar da suke takawa wajen haskaka ayyukan shirin, yana mai cewa gudunmawarsu ta taimaka ƙwarai wajen isar da muhimman saƙonni ga al’umma.

Ya ƙara da cewa shirin ya horar da wasu ‘yan jarida biyar, ciki har da waɗanda daga bisani aka karrama su a matsayin fitattun ‘yan jarida masu ba da gudunmawa wajen yaɗa bayanai kan sauyin yanayi a jihar.

A ƙarshe, ya miƙa wannan karramawa ga Gwamna Inuwa Yahaya da shugabannin shirin a matakin ƙasa da jiha, ciki har da Dokta Joy Iganya Agene da Abdulhamid Umar, bisa irin gudunmawar da suke bayarwa wajen ƙarfafa juriya ga sauyin yanayi da kare muhalli a Jihar Gombe.

By ukarofi