Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Jam’iyyar APC a Jihar Zamfara yau Asabar ta zabi sabbin Shugabannin ta yayin da Kabiru Moyi Birnin Magaji ya zama shugaban jam’iyyar.
Sauran zaɓaɓɓun jami’an sun haɗa da, Hon. Ibrahim Danmaliki a matsayin Sakatare, Hon. Ibrahim Muhammad a matsayin Sakataren yaɗa labarai, Hon. Yusuf Idris a matsayin Mai Binciken Kudi, Hon. Sani Musa Mataimakin Shugaban Jam’iyya, Barista Samaila Mainasara mai ba da shawara kan harkokin shari’a, Abubakar Shehu, ma’aji da Hajiya Rabi Madawaki, shugabar mata da Abdullahi Dan’azumi a matsayin shugaban matasa da sauransu.
A cikin saƙon fatan alheri, shugaban kula da zaɓen, kuma mataimakiyar gwamnan Jihar Kaduna, Hadiza Sabuwa Balarabe ta buƙaci sabbin shugabannin da su tabbatar da adalci wajen sauke nauyin da ke kan su.
Ta sake jaddada haɗin kai tsakanin ‘yan jam’iyyar APC a jihar a matsayin babban abun bai wa fifiko.
“Da haɗin kai, APC za ta yi kyau kuma ta samu nasara a 2027 ba kawai a jihar ba har ma da ƙasa baki ɗaya. Ta ce
Wani mai ruwa da tsaki a jam’iyyar, Dakta Sani Abdullahi Shinkafi, a saƙon sa na fatan alheri, ya yi kira ga dukkan magoya bayan jam’iyyar APC da su yi gangami don goyon bayan takarar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da gwamna Dauda Lawal a 2027.
Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na ƙasa a yankin Arewa, yayi maraba da gwamna Dauda Lawal zuwa APC, yana mai cewa sauya shekarsa zai kawo nasarar APC a 2027 a jihar Zamfara.
Yayi Kira ga sabbin Shugabannin da su tabbatar anyi aiki kafaɗa da kafaɗa da duk yayan jam’iyyar don cimma nasarar da ake buƙata.
Gwamna Dauda Lawal a cikin jawabinsa, ya yi kira ga sabbin shugabannin jam’iyyar da su ɗauki kowane memba a matsayin abu guda, su kuma tabbatar da adalci, riƙon amana da gaskiya a lokacin da suke kan mulki.
“Gwamnatina za ta ba da dukkan goyon bayan da ake buƙata ga shugabannin APC kuma ina kira ga sabbin shugabannin da su mai da hankali kan ci gaban jam’iyyar a jihar Zamfara”. Gwamna Lawal ya ce
A jawabinsa na amincewa, shugaban jam’iyyar APC na jihar, Kabiru Moyi Birnin Magaji, ya yi alƙawarin yin aiki tare da membobin zartarwa da duk masu ruwa da tsaki don tabbatar da nasarar jam’iyyar a jihar.
Zan gudanar da aiki kafaɗa da kafaɗa da dukkanin magoya bayan jam’iyyar da masu ruwa da tsaki kuma ƙofar mu a buɗe take don amsar shawarwari don haɓaka jam’iyyar mu ta APC da kuma tabbatar da nasararta a 2027.” Moyi ya ce
