Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Mai Alfarma Sarkin Musulmin Nijeriya, Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya shawarci ’yan Nijeriya da su yi taka-tsantsan tare da tantance alƙawuran ’yan siyasa kafin su yanke shawarar wanda za su mara wa baya a babban zaɓen ƙasar na 2027.
Sarkin ya kuma gargaɗi ’yan siyasa da su guji mayar da matsalar tsaro da sauran ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta tamkar kayan kamfen a lokacin yaƙin neman zaɓe, yana mai cewa ya kamata su fi mayar da hankali kan batutuwan da za su taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban ƙasa.
Sarkin Musulmin ya bayyana hakan ne a ranar Litinin lokacin da ya karɓi tawagar Majalisar Kamfen ta Jam’iyyar APC ta 2027, ƙarƙashin jagorancin Darakta-Janar ɗinta, Sanata Abdul-Aziz Yari Abubakar, a fadarsa da ke Sakkwato.
Ya buƙaci masu zaɓe da su saurari alƙawuran ’yan siyasa da kyau a lokacin yaƙin neman zaɓe, sannan su yi zaɓin da suka yi imanin zai fi amfani da su da kuma ƙasar baki ɗaya.
Haka kuma, Sarkin ya yi kira ga jam’iyyun siyasa da ’yan takararsu da su gudanar da kamfen cikin lumana, wanda zai ta’allaƙa kan manufofi da batutuwan da suka shafi rayuwar al’umma, tare da mutunta zaɓin masu kaɗa ƙuri’a.
Sai kuma ya ce, ya kamata ’yan siyasa su gudanar da harkokinsu ta yadda za su ƙara ƙarfafa haɗin kan ƙasa da samar da ci gaba, maimakon amfani da bambance-bambancen siyasa wajen raba kan al’umma.
Sarkin ya bayyana cewa babu wata gwamnati a duniya da za ta iya kawar da matsalar rashin tsaro da talauci gaba ɗaya, sai dai gwamnati na da damar ɗaukar matakan da za su rage illolinsu da tasirinsu ga jama’a.
Ya yi wa mambobin Majalisar Kamfen ta APC fatan samun nasara, tare da addu’ar Allah Ya ci gaba da tabbatar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da kyakkyawan shugabanci a Nijeriya.
Tun da farko, Sanata Abdul-Aziz Yari ya ce tawagar ta kai ziyarar ne domin neman shawarwari, jagoranci na uba da kuma addu’ar Sarkin Musulmi gabanin babban zaɓen 2027.
Yari ya ce Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu tun kafin ya zama shugaban ƙasa ya nuna ƙudirin sa na taimaka wa ci gaban Arewa da Nijeriya, ta hanyar tallafa wa shugabanni da kuma wasu tsare-tsaren ci gaba.
Ya ce gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin APC na da nasarori da dama da take son gabatar wa ’yan Nijeriya, musamman waɗanda aka samu a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu.
A cewarsa, gwamnatin ta ci gaba da mai da hankali wajen inganta zaman lafiya, haɗin kai da fahimtar juna a tsakanin al’ummar ƙasar.
Yari ya tabbatar wa Sarkin Musulmi cewa jam’iyyar za ta gudanar da yaƙin neman zaɓe cikin lumana, tare da neman ci gaba da goyon bayan Sarkin da addu’o’insa kafin gudanar da zaɓen.
Shi ma Gwamnan Jihar Sakkwato, Dakta Ahmed Aliyu, ya ce tsarin shirye-shiryen babban zaɓen 2027 ya fara gudana a faɗin ƙasar, bisa jadawalin lokaci da ƙa’idojin da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta tsara.
Gwamnan ya bayyana cewa Majalisar Kamfen ta ga ya dace ta kai ziyarar tun da wuri ga Sarkin Musulmi saboda matsayinsa na jagoran al’ummar Musulmi da kuma irin gudunmawar da ya daɗe yana bayarwa wajen tabbatar da zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.
Daga cikin sauran waɗanda suka raka tawagar akwai Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris; Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal; Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko; Sanata Adamu Aliero; Sanata Ali Modu Sheriff; tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Masari; da tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, da sauran manyan ’yan jam’iyyar.
