*Mun shirya tsaf don tunkarar zaɓen 2027 – INEC
*Za mu sa ido kan take-takenku – Alƙalin-alƙalai ga masu shari’a
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Babbar Alƙalin Alƙalan Nijeriya (CJN), Mai Shari’a Kudirat Motomori Kekere-Ekun, ta gargaɗi alƙalan da za a naɗa domin zama a kotunan sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe da su tabbatar da cewa sun kasance masu gaskiya da adalci, tana mai cewa za a sa ido sosai tare da bibiyar yadda suke gudanar da ayyukansu.
CJN ta kuma gargaɗi lauyoyi da kada su yi amfani da ’yancinsu na sukar hukuncin kotu ko yadda ake gudanar da shari’a wajen kai wa alƙalai hari, karkatar da bayanan abin da ya faru a kotu da gangan, ko ƙoƙarin matsa wa kotu lamba ta hanyar amfani da ra’ayin jama’a.
Ta yi wannan gargaɗin ne a ranar Laraba yayin ƙaddamar da sabuwar shekarar shari’a ta 2026/2027 ta Kotun Masana’antu ta ƙasa ta Nijeriya (NICN). Kekere-Ekun ta bayyana cewa wasu daga cikin alƙalan kotun na iya samun damar zama mambobin Kotunan ƙorafe-ƙorafen Zaɓe, tana mai cewa irin wannan aiki na buƙatar cikakken rashin son kai, haƙuri da nesantar duk wani abu da zai iya jefa shakku kan adalcin alƙali.
Gargaɗjn nata ya zo ne yayin da ake shirye-shiryen babban zaɓen 2027, wanda ya rage ƙasa da kwanaki 100 kafin gudanar da shi. Ta ce, kotuna na buƙatar kasancewa cikin shirin ilimi da ƙwarewa domin tunkarar ƙalubalen zamani, tare da tabbatar da cewa hukuncin da suke yankewa ya dogara kacokan kan Kundin Tsarin Mulki, dokokin da suka dace, hukuncin kotuna da ya zama abin dogaro da kuma ingantattun ƙa’idojin yanke hukunci.
CJN ta kuma buƙaci lauyoyi da su guji kai ƙara iri ɗaya a kotuna daban-daban, lamarin da ka iya haifar da hukuncin kotu masu karo da juna. Ta ce irin wannan ɗabi’a na iya rage amincewar jama’a ga tsarin shari’a tare da jefa ɓangaren shari’a cikin abin kunya.
Da take magana kan rawar da wasu alƙalan kotun za su iya takawa a lokacin zaɓe, ta ce, “Yayin da muke tunkarar wani sabon kakar zaɓe, waɗannan nauyin da ke kanku sun ƙara zama masu muhimmanci. Wasu daga cikin ku na iya, bisa tanadin Kundin Tsarin Mulki da dokokin da suka dace, samun damar zama mambobin kotunan sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe.
“A wannan matsayi, za a buƙaci ku yanke hukunci kan taƙaddamar siyasa mai matuƙar muhimmanci wadda za ta jawo hankalin jama’a sosai. Saboda haka, irin wannan aiki na buƙatar ƙarin matakin rashin son kai, kame kai da nisantar duk wata alaƙa da za ta iya shafar hukunci. Ko kuna zaman kotu ko kuna aikin kotun ƙorafe-ƙorafen zaɓe, dole ne ku kasance masu sanin cewa za a sa ido sosai kan halayenku.
“Dole ne ku tabbatar da cewa babu wani abu cikin alaƙarku da mutane, hulɗarku da jama’a ko wasu halayenku da zai haifar da tunanin cewa kuna da alaƙa da wata ƙungiyar siyasa ko kuma kun riga kun karkata zuwa wani ɓangare.
“ƙungiyar Lauyoyi ba za ta taɓa zama hanyar da za a yi amfani da ita wajen murɗe tsarin shari’a domin cimma muradun siyasa ko dabarun wani ɓangare ba. Doka ce ke ƙayyade kotun da ya kamata a kai ƙara, ba wai zato ko tunanin cewa wani alƙali ko wata kotu ce za ta fi ba da damar samun nasara ba.”
Yayin da take magana kan matakin wasu lauyoyi na sukar alƙalai da hukuncin kotu, Kekere-Ekun ta ce ’yancin sukar hukunci ko tsarin shari’a ba ya ba da damar kai wa alƙalai hari kai tsaye. Ta ce, irin wannan ’yanci bai haɗa da cin mutuncin alƙalai, karkatar da bayanan abin da ya gudana a kotu da gangan ko ƙoƙarin matsa wa kotu lamba ta hanyar ra’ayin jama’a ba. Ta ƙara da cewa, idan akwai sahihan aorafe-ƙorafe kan halayen wani alƙali, akwai hanyoyin hukuma da ya kamata a bi domin gabatar da irin waɗannan ƙorafe-ƙorafen.
Babbar mai shari’ar (CJN) ta kuma yi kira ga lauyoyi da su kasance masu ƙwarewa yayin gudanar da shari’o’in da suka shafi siyasa, tana mai cewa bai kamata a riƙa kai ƙara kotuna ko rassa daban-daban da fatan samun hukuncin da ya fi dacewa da wani ɓangare ba.
Mun shirya tsaf, inji shugaban INEC:
Bugu da ƙari, a wani ci gaban makamancin wannan, Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, SAN, ya ce, hukumar ta kammala shirye-shiryen gudanar da sahihin zaɓe a 2027 tare da tabbatar da ba ta goyi bayan wani ɗan takara ko wata jam’iyya ba.
Amupitan ya bayyana hakan ne ranar Alhamis a Legas, yayin gabatar da babban jawabi a taron shekara-shekara na 10 na ƙungiyar Masu Buga Labaran Intanet na Kamfanoni (GOCOP), mai taken: “Zaɓen 2027: Amincewa, Gaskiya da Nauyin da Ya Rataya a Kan Kowa.”
Ya ce, zagayen zaɓen 2027 zai fara ne da zaɓen Shugaban ƙasa da na Majalisar Dokoki ranar Asabar, 16 ga Janairun 2027, sannan a gudanar da zaɓen gwamnoni da na Majalisun Dokokin Jihohi ranar 6 ga Fabrairu, 2027.
Ya ƙara da cewa, yayin da kwanaki 98 suka rage kafin fara zaɓen, INEC ta samu gagarumar nasara wajen aiwatar da jadawalin ayyukan da ta tsara.
A cewarsa, hukumar ta fitar da sabon jadawalin zaɓe da ayyukan da za a gudanar a ranar 26 ga Fabrairun 2026, wanda ya ƙunshi muhimman ayyuka 14 da doka ta tanada, kuma a yanzu tana kammala na tara.
Ya ce, an fara aiwatar da jadawalin a sassan hedikwatar hukumar guda 23, ofisoshin jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya Abuja, da kuma ofisoshin ƙananan hukumomi 774, waɗanda ke kula da sama da rumfunan zaɓe 176,000.
Shugaban INEC, wanda Kwamishinan Zaɓe na Mazaunin Jihar Legas, Farfesa Ayonami Salami, ya wakilta, ya bayyana cewa adadin masu rajista a kundin masu zaɓe na Nijeriya ya kai wani sabon tarihi na miliyan 103, bayan kammala matakai uku na Ci gaba da Rajistar Masu Zaɓe (CɓR).
A mataki na farko, daga 25 ga Agusta zuwa 10 ga Disamban 2025, an yi wa sabbin masu zaɓe 2,611,266 rajista; yayin da mataki na biyu, daga 5 ga Janairu zuwa 17 ga Afrilun 2026, ya ƙara masu zaɓe 4,121,835.
A mataki na uku, wanda aka gudanar daga 11 ga Mayu zuwa 26 ga Yulin 2026, an samu sabbin masu zaɓe 3,867,997. Ya ce hukumar ta kammala baje kolin kundin farko na masu zaɓe domin jama’a su gabatar da ƙorafe-ƙorafe da gyare-gyare, yayin da ake kammala haɗa bayanan ta hanyar Tsarin Gano ɗan Adam ta Bayanai na Na’ura Mai ƙwaƙwalwa (ABIS) domin kawar da maimaitattun bayanan masu zaɓe.
Shugaban INEC ya sanar da cewa za a fara rabon Katin Zaɓe na Dindindin (PɓC) a faɗin ƙasar ranar Juma’a, 9 ga Oktoba, 2026, ta amfani da sabuwar fasahar Printable PɓC, a cibiyoyin ƙananan hukumomi da wuraren rajista.
Ya buƙaci mambobin GOCOP da su yi amfani da kafafen yaɗa labaransu wajen wayar da kan jama’a da ƙarfafa su su je su karɓi katunan zaɓensu.
Dangane da shirye-shiryen fasaha, Amupitan ya ce an inganta na’urorin Bimodal ɓoter Accreditation System (BɓAS), tare da daidaita batir, ƙara musu ƙarfin aiki da kuma inganta manhajojinsu domin daƙile kwaikwayon wani mai zaɓe.
Ya ce ana kuma gudanar da cikakken binciken na’urorin a faɗin ƙasa tare da sayen wasu sababbin na’urori. Hukumar ta kuma inganta tsarin tabbatar da sahihancin sakamakon zaɓe ta hanyar eEC8A, wanda ke mayar da takardar sakamakon rumfar zaɓe, wato Form EC8A, zuwa tsarin dijital nan take bayan kammala ƙirga ƙuri’u.
A cewarsa, tsarin na sanya sa hannun dijital mai kariya ga sakamakon sannan ya aika shi zuwa wani dandali na jama’a, domin ba da damar bibiyar sakamakon daga matakin rumfar zaɓe zuwa matakin ƙarshe. Ya ce an gwada tsarin a zaɓukan cike gurbi da aka gudanar kwanan nan a Babban Birnin Tarayya Abuja, Ekiti da Osun.
Haka kuma, ya ce INEC ta haɗa kayan aikin binciken bayanai da ke amfani da AI da kuma katangar tsaro ta yanar gizo mai matakai da dama, tare da haɗin gwiwar kamfanonin Google da Microsoft, domin kare tsarin hukumar daga hare-haren kutse da na Distributed Denial-of-Serɓice (DDoS).
Amupitan ya ce hukumar ta fara sayen kayayyakin zaɓe marasa muhimmanci tun da wuri, kuma ana ci gaba da rarraba su zuwa jihohi. Ya ce, an kuma sayi sababbin motocin ɗaukar kaya domin magance matsalolin sufuri a wurare masu wahalar isa, ciki har da yankunan da ke da koguna da kuma al’ummomin kan iyakoki. Ya ƙara da cewa, an kafa tsarin gudanar da ayyuka na bai ɗaya wanda ke ba hukumar damar bibiyar motsin kayayyakin zaɓe da wuraren da aka adana su kai tsaye.
Hukumar ta kuma fara gudanar da Binciken Shirye-shiryen Yankuna a shiyyoyin siyasa shida na ƙasar domin tantance kayan aiki, sufuri da matakan mayar da martani ga yanayin gaggawa. An riga an kammala irin wannan bincike a Kudu maso Yamma da Arewa maso Yamma.
Amupitan ya kuma gargaɗi ma’aikatan hukumar da su guji nuna goyon baya ga kowace jam’iyya ko ɗan takara. Ya jaddada cewa, bisa Sashe na 26 na Dokar Zaɓe ta 2026, dole ne kowane jami’in zaɓe ya rantse kan yin aiki cikin cikakkiyar rashin nuna son kai, yana mai cewa nuna ɓangaranci ko sakaci na iya janyo korar jami’i daga aiki da kuma gurfanar da shi gaban kotu.
