Yayin da shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen shekarar 2027 ke ƙara ɗaukar zafi, shugabannin haɗin gwiwar Majalisar ƙasa ta Addinai (NIREC), wato Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar III, da Shugaban ƙungiyar Kiristocin Nijeriya (CAN), Archbishop Daniel Okoh, sun yi gargaɗi ga shugabannin addinai kan amfani da mimbari, coci-coci, masallatai da sauran dandalan addini wajen rura wutar siyasa ko tayar da rikicin addini a lokacin da ake tunkarar zaɓe.
Haka kuma, Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Sanata George Akume; Babban Sakataren NIREC, Farfesa Cornelius Afebu Omonokhua; da Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Ƙasa (EFCC), Ola Olukoyede, sun buƙaci shugabannin addinai da su zama masu jagorantar zaman lafiya, riƙon amana, sulhu da haɗin kan ƙasa.
Wannan kira ya zo ne bayan sanya hannu kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya ta ƙasa ta farko a ranar 18 ga Agusta, 2026, wadda jam’iyyun siyasa, ’yan takarar shugaban ƙasa da na Majalisar Dokoki suka rattaba hannu a kai. Yarjejeniyar ta nuna cewa a hukumance an shiga wani sabon mataki na shirye-shiryen yaƙin neman zaɓen 2027.
Yarjejeniyar ta tanadi cewa waɗanda suka sanya hannu a kanta za su gudanar da kamfen bisa batutuwa da manufofi, tare da kauce wa tashin hankali, kalaman ƙiyayya, yaɗa bayanan ƙarya, kai wa ’yan takara hari da cin zarafi da kuma duk wani mataki da ka iya lalata tsarin zaɓe.
Shugabannin sun bayyana waɗannan matsayai ne a Abuja a ranar Talatar makon jiya, yayin taron majalisar NIREC na biyu na shekarar 2026, wanda aka gudanar ƙarƙashin taken: “Ci Gaban Addini Mai Ma’ana a Nijeriya.”
Sarkin Musulmi ya buƙaci shugabannin Musulmi da Kiristoci da su guji mayar da wa’azi, addu’o’i da tarukan addini zuwa wuraren kai hari ga shugabannin siyasa, rarrabuwar kawuna ko yin kalaman da za su iya tayar da hankali kan ’yan takara da masu riƙe da muƙaman gwamnati.
Ya ce yayin da aka shiga kakar yaƙin neman zaɓen 2027, wajibi ne shugabannin addinai su yi taka-tsantsan da irin kalaman da suke furtawa a majami’u, masallatai da sauran wuraren ibada.
Sarkin Musulmin ya kuma buƙaci shugabannin addinai da mabiyansu su riƙa yi wa Shugaban ƙasa, gwamnoni da ’yan Majalisar ƙasa addu’a, maimakon yin addu’ar faɗuwarsu ko gazawarsu.
A cewarsa, ko da mutum yana ganin shugabanni ba sa gudanar da mulki yadda ya kamata, ya kamata a ci gaba da yi musu addu’a domin Allah Ya shiryar da su, Ya kuma gyara al’amuransu.
Haka kuma, Sarkin Musulmin ya yi gargaɗi kan mayar da wuraren ibada dandamalin yaƙin neman zaɓe, yana mai cewa ya kamata shugabannin addinai su zama masu ƙarfafa zaman lafiya da kuma wayar da kan jama’a kan muhimmancin shiga harkokin zabe cikin lumana da sanin ya kamata.
Ya kuma yi kira ga shugabannin addinai da su riƙa tattaunawa cikin gaskiya da juna, tare da guje wa yaɗa bayanan ƙarya bayan tarukan da ake gudanarwa tsakanin mabiya addinai daban-daban. Ya ce tattaunawa tsakanin addinai na daga cikin ginshiƙan da za su taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban Nijeriya.
Sarkin Musulmin ya kuma buƙaci shugabannin addinai su ɗauki tsauraran matakai wajen yaƙi da cin hanci da rashawa, tare da mara wa EFCC baya wajen hukunta duk wanda aka samu da laifi, ba tare da la’akari da addininsa ko matsayinsa na siyasa ba.
Ya yi gargaɗin cewa bai kamata a yi amfani da kuɗaɗen da aka samu ta hanyar cin hanci da rashawa wajen gudanar da ayyukan addini, ciki har da aikin Hajji da sauran ibadu ba, yana mai jaddada cewa babu wanda ya kamata ya kasance sama da doka.
A nasa ɓangaren, Akume, wanda ya wakilci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a taron, ya buƙaci shugabannin addinai da na gargajiya su yi amfani da matsayinsu wajen ƙarfafa zaman lafiya da hana siyasa zama sanadin rikicin addini ko ƙabilanci.
Ya ce a yayin kamfen ɗin da ke tafe, ya kamata shugabannin addinai su fito da saƙo bayyananne cewa siyasa ta dace da akwatin zaɓe, ba a gaban bagaɗi ko cikin masallaci ba.
Akume ya kuma buƙaci shugabannin addinai su hana ’yan daba masu alaƙa da siyasa amfani da wuraren ibada a matsayin mafaka, tare da ƙarfafa Kiristoci da Musulmi su shirya addu’o’in haɗin gwiwa da sauran shirye-shiryen zaman lafiya kafin zaɓen 2027.
Tun da farko, Shugaban CAN, Archbishop Daniel Okoh, ya ce cibiyoyin addini na da babbar alhakin amfani da tasirinsu wajen gina zaman lafiya, sulhu da haɗin kan ƙasa.
Ya ce matsalolin da Nijeriya ke fuskanta, waɗanda suka haɗa da rashin tsaro, talauci, rashin aikin yi, rashin daidaito tsakanin jama’a, rikice-rikicen al’umma da raguwar amincewar jama’a ga hukumomi, na buƙatar haɗin kan kowa ba tare da la’akari da addini ko muradun wani ɓangare ba.
Okoh ya ce ya kamata shugabannin addinai su tambayi kansu irin Nijeriyar da suke taimakawa wajen ginawa ta hanyar kalamansu, ayyukansu da kuma tasirin da suke da shi a cikin al’umma.
Ya kuma yi kira ga coci-coci da masallatai da su yi amfani da matsayinsu wajen gina gadoji tsakanin jama’a maimakon ƙara katangar rarrabuwar kai, tare da fifita sulhu a kan shakku da rashin yarda.
Waɗannan kiraye-kirayen na manyan shugabannin addini da na gwamnati sun sake jaddada muhimmancin raba harkokin siyasa da wuraren ibada yayin da Nijeriya ke shirin tunkarar zaɓen 2027.
Musamman, gargaɗin Sarkin Musulmi da Shugaban CAN ya zo ne a lokacin da ake buƙatar a yi hattara da maimaita abubuwan da suka faru a zaɓen 2023, lokacin da batutuwan siyasa suka kutsa sosai cikin harkokin addini.
A wancan lokaci, batun tikitin shugaban ƙasa na Musulmi da Musulmi ya zama babban batu a yaƙin neman zaɓe, inda wasu ’yan siyasa da masu wa’azi suka yi amfani da batun wajen ƙarfafa goyon baya ko adawa da ’yan takara bisa tushen addini. Hakan ya taimaka wajen zurfafa rarrabuwar kai da rashin jituwa tsakanin wasu mabiya manyan addinan ƙasar biyu.
Saboda haka, gargaɗin da shugabannin NIREC suka yi ya zo a daidai lokacin da ake buƙatar a sake duba yadda ake amfani da addini a harkokin siyasa. Ya kamata ’yan siyasa su gane cewa coci da masallaci wuraren ibada ne, ba dandamalin yaƙin neman zaɓen jam’iyya ko ’yan takara ba.
Haka nan, shugabannin addinai suna da babban nauyi na kare martabar wuraren ibada daga rikicin siyasa. Tasirin da suke da shi a tsakanin miliyoyin mabiyansu zai iya zama wata babbar hanya ta gina zaman lafiya da haɗin kai, idan aka yi amfani da shi cikin gaskiya da kishin ƙasa.
Siyasa ta dace a yi ta bisa manufofi, tsare-tsare da ra’ayoyin da suka shafi rayuwar jama’a. Ya kamata ’yan takara su nemi ƙuri’un jama’a ta hanyar bayyana abin da suke son yi wa ƙasa, maimakon neman samun goyon baya ta hanyar tsoratarwa, amfani da addini ko tayar da ƙabilanci.
A lokaci guda, Majalisar Dokoki ta ƙasa na iya yin nazari kan yadda za a samar da ingantaccen tsarin doka da zai kare ’yancin addini, tare da hana amfani da wuraren ibada ko tasirin addini wajen haifar da rikicin siyasa, addini ko na ƙabilanci.
Nijeriya na buƙatar zaɓe mai cike da gasa, amma gasa wadda ba za ta raba kan jama’a ba. Wuraren ibada kuma su kasance wuraren da ake koyar da zaman lafiya, gaskiya, haƙuri da tausayi, ba wuraren da ake rura wutar siyasa da rarrabuwar kai ba.
