Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano
Makarantar Kimiyya da Fasaha da ke ƙaramar Hukumar Dawakin Kudu ta gudanar da taron haɗin gwiwa da iyayen ɗalibai domin tattauna batutuwan da suka shafi ci gaban karatu, tarbiyya da kyautata harkokin makarantar.
Taron ya samu halartar iyaye da masu ruwa da tsaki, inda aka tattauna muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin makaranta da iyaye wajen tabbatar da samun ingantaccen ilimi da tarbiyya ga ɗalibai.
Tun da fari, Shugaban ƙungiyar Iyayen da Malamai ta makarantar (PTA), Alhaji Auwal Iliyasu, ya jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin iyaye da makaranta, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen inganta harkar koyo da koyarwa a makarantar.
Alhaji Auwal Iliyasu ya bayyana irin nasarorin da ƙungiyar ta samu, waɗanda suka haɗa da samar da rajista da yin jarabawar NECO da NABTEB, da kuma samar da kujerun zama ga ɗalibai.
Ya kuma yabawa wasu mutane da suke ba ƙungiyar gudunmawa, ciki har da Alhaji Aminu Ahmed Dawaki, Alhaji Umar Auta Kore, Alhaji Ibrahim Aliyu Yayale, kamfanin shinkafa na UMZA, kamfanin samar da gine-gine da hanyoyi na H@H, da sauran masu taimaka wa makarantar ta hanyoyi daban-daban domin ci gaban ilimi a yankin.
Da yake jawabin godiya, shugaban makarantar, Malam Bello Isyaku, ya bayyana cewa makarantar za ta ci gaba da yin aiki kafada da kafada da ƙungiyar iyaye da malamai domin samar da kyakkyawan yanayi na koyo da koyarwa, haɗi da kulawa da tarbiyyar ɗalibai.
A nasa jawabin, wakilin Babban Sakataren Hukumar Kula da Makarantun Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano (STEB), wanda Daraktan Kula da Ayyuka na Musamman, Malam Salisu Auwal, ya wakilta, ya yaba da yadda makarantar ke haɗa kai da iyaye.
Ya ƙarfafa iyaye da malamai da su ci gaba da ba ɗalibai cikakken goyon baya domin samun ingantaccen ilimi da ƙwarewar sana’o’i.
An kuma tattauna muhimman batutuwa da suka shafi walwala da ci gaban ɗalibai, bin dokokin makaranta, halartar karatu a kan lokaci da kuma muhimmancin koyon sana’o’in fasaha domin ɗalibai su zama masu dogaro da kansu a nan gaba.
Mahalarta taron sun jaddada aniyar ci gaba da haɗin gwiwa tsakanin makaranta, iyaye da hukumomin ilimi domin inganta harkokin karatu da ci gaban makarantar.
